Tambuwal ya gargadi magoya bayan jam'iyyar PDP da su kauracewa yin gulma da tsugudidi

Tambuwal ya gargadi magoya bayan jam'iyyar PDP da su kauracewa yin gulma da tsugudidi

- Tambuwal ya gargadi magoya bayan jam'iyyar PDP a jihar, da su kauracewa yin gulma da tsugudidi mai makon mayar da hankali wajen yada nasarorin da jam'iyyar ta samu

- Ya kuma kara bata tabbacin yunkurin gwamnatinsa na bude kofa ga duk wasu shawarwari, da za su taimakawa PDP wajen samun nasara a babban zaben 2019 da ke gabatowa

- Tun farko, tsohon gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Attahiru Bafarawa ya ce babu wani sabani tsakaninsa da Gwamna Tambuwal, ya ce jita jita ce kawai ake yadawa

Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal ya gargadi magoya bayan jam'iyyar PDP a jihar, da su kauracewa yin gulma da tsugudidi mai makon mayar da hankali wajen yada nasarorin da jam'iyyar ta samu a jihar.

Gwamnan ya yi wannan gargadin ne a wani taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar PDP da ya gudana a cikin gidan gwamnatin jihar Sokoto.

Tambuwal ya jaddada cewa an shirya taron ne don warware kullin da wasu marasa kishin jam'iyyar ke kullawa, yana mai nuni da cewa akwai jita jitar da ke yawo don cusa wasi wasi a zukatan jama'ar jihar Sokoto, tare da bata sunan PDP.

Don haka gwamnan, ya jaddada cewa har yanzu akwai hadin kai a tsakanin shuwagabannin jam'iyyar a jihar da kuma kyakkyawan makoma.

KARANTA WANNAN: Gwamnan Cross River, Ayade ya caccaki PDP a bainar jama'a kan zaben fitar da gwani

Tambuwal ya gargadi magoya bayan jam'iyyar PDP da su kauracewa yin gulma da tsugudidi
Tambuwal ya gargadi magoya bayan jam'iyyar PDP da su kauracewa yin gulma da tsugudidi
Asali: Depositphotos

Ya kuma kara bata tabbacin yunkurin gwamnatinsa na bude kofa ga duk wasu shawarwari, da za su taimaka wajen baiwa jam'iyyar PDP nasara a matakan shugabanci daban daban a babban zaben 2019 da ke gabatowa.

Tun farko, tsohon gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Attahiru Bafarawa ya kara bada tabbacin hadin kan jam'iyyar PDP a jihar Sokoto.

Tsohon gwamnan wanda ya yi shugananci har na shekaru 8, ya ce babu wani sabani tsakaninsa da Gwamna Tambuwal, inda ya kara da cewa jita jita ce kawai ake yadawa, kana ya roki al'ummar jihar Sokoto da su ci gaba da goyon bayan Gwamna Tambuwal a kokarinsa na dai-daita tattalin arzikin jihar.

Bafarawa ya kara da cewa za su tabbata sun ja hankulan dandazon jama'a don fitowa kwansu da kwarkwatarsu, don zabar yan takarar PDP a zabe mai zuwa.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel