Idan hagu ta ki, sai ka koma dama don haka na bar APC na dawo PDP – Sanata Kwankwaso

Idan hagu ta ki, sai ka koma dama don haka na bar APC na dawo PDP – Sanata Kwankwaso

- Kwankwaso yace Jam’iyyar APC ta karbe abubuwan da su ke da shi

- Sanatan kuma yace Gwamnati ba tayi masu sakayya da komai ba 2019

- Tsohon Gwamnan yayi magana game da 2019 a lokacin da ya je Kano

Idan hagu ta ki, sai ka koma dama don haka na bar APC na dawo PDP – Sanata Kwankwaso
Kwankwaso yace babu wanda zai iya ja da 'Yan Kwankwasiyya da Jam’iyyar PDP a Kano
Asali: Facebook

Mun samu labari cewa tsohon Gwamnan Jihar Kano Injiniya Rabiu Kwankwaso ya fito yayi magana game da dalilin da ya sa ya fice daga Jam’iyyar APC mai mulki ya kuma koma Jam’iyyar sa ta asali watau PDP mai adawa.

Sanatan na Kano ta tsakiya ya bayyana wannan ne a lokacin da ya kai wata ziyara Jihar Kano kwanan nan inda ya gana da Dattawa da ‘Yan siyasa da sauran Mutanen Jihar. Sanatan dai ya dauki lokacin rabon sa da Jihar ta sa.

Tsohon Gwamnan ya nuna cewa Jam’iyyar APC ba tayi masu adalci ba, inda yace APC ta karbe duk abubuwan da su ka mallaka na siyasa amma kuma su kare a tutar babu bayan zaben 2015, domin kuwa ba saka masu da komai ba.

KU KARANTA: Atiku, Saraki da Kwankwaso sun yi wani zama domin shiryawa 2019

Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso ua bayyana wannan ne lokacin da ya gana da Mutanen Yankin Takai da kuma Sumaila a gidan sa inda ya nemi su yi kokarin ganin Jam’iyyar PDP ta kai labari a zaben 2019 a Kauyukan su na Kano.

Tsohon Gwamnan na Kano ya kuma caccaki ‘Dan takarar PRP Salihi Sagir Takai wanda ya bar PDP. Kwankwaso yace Takai ba zai ko ina ba a 2019 domin babu yadda za ayi ya kara da ‘Yan Kwankwasiyya da sauran ‘Yan PDP.

Sanatan ya kuma bayyana cewa yayi wa Takai tayin kujerar Sanata da kuma Mataimakin Gwamna amma ya watsar. Kwankwaso yace irin su Ibrahim Shekarau dai sun dage su na neman kujerar ta sa, har yayi izgila ga gemun sa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel