Ana satar jama’a ana garkuwa da su a Katsina amma Gwamna Masari yana rawa da Mawaka Inji PDP

Ana satar jama’a ana garkuwa da su a Katsina amma Gwamna Masari yana rawa da Mawaka Inji PDP

Mun ji cewa Babbar Jam’iyyar adawa ta PDP na reshen Jihar Katsina ta nemi Gwamnan Jihar watau Rt. Hon. Aminu Bello Masari ya sauka daga kujerar sa a dalilin kashe-kashe da satar jama’a da ya barke a Jihar.

Ana satar jama’a ana garkuwa da su a Katsina amma Gwamna Masari yana rawa da Mawaka Inji PDP
An zargi Gwamnan Katsina da sakaci da rayukan Jama’a a Jihar
Asali: Twitter

Shugaban Jam’iyyar PDP na Jihar Katsina Hon. Salisu Yusuf Majigiri ya nemi Gwamna Aminu Bello Masari ya ajiye kujerar sa bayan an sace mutane kusan 10 a cikin Garin Batsari kwanan nan. Daga cikin wadanda aka sace har da wasu Kansiloli.

Salisu Yusuf Majigiri ya zargi Gwamna Masari da sakaci a matsayin sa na wanda aka zaba domin ya kare rayuka da dukiyar al’umma. Majigiri ya bayyanawa manema labarai cewa Masari ya gaza shawo kan matsalar tsaro a Jihar ta Katsina.

KU KARANTA: 'Yan Boko Haram sun koma satar dabbobi a Jihar Borno

Shugaban Jam’iyyar adawar yace a daidai lokacin da ake sata da kashe-kashen mutane, Mai Girma Gwamnan ya gayyaci Mawaka daga Kano zuwa Katsina inda aka rika cashewa da kade-kade da raye yayin da ake cikin wani hali a fadin Jihar.

Alhaji Majigiri ya bayyana cewa ko dai Gwamnan Jihar ya nemawa kan sa sauki yayi murabus tun yanzu a dalilin gazawar sa ko kuma PDP ta tika sa da kasa a zaben 2019. Jam’iyyar tace gara dai Gwamnan ya nemawa Jihar sauki tun yanzu.

A cewar Shugaban Jam’iyyar adawar, ba harkar tsaro ba ne a gaban Gwamna Masari domin kuwa da ya maida hankali wajen tsare ran mutanen Jihar. Yanzu dai ana kara samun yawan kashe-kashe da satar Bayin Allah ana garkuwa da su a Jihar ta Katsina.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng