EFCC ta shiga Kotu ta Tuoya Omatsuli bisa zargin satar Biliyan 3.6
Mun samu labari cewa Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa tana karar tsohon Shugaban Hukumar NDDC ta Neja-Delta da satar kudi a babban Kotun Tarayya da ke Garin Legas.
A jiya Alhamis 8 ga Watan Nuwamban nan ne Hukumar EFCC ta gurfanar da Tuoyo Omatsuli wanda ya taba rike shugaban Hukumar da ke kula da cigaban Yankin Neja-Delta da kuma wani Franci Momoh a gaban babban Kotu.
EFCC na reshen Legas tana zargin tsohon Shugaban Hukumar na NDDC Tuoyo Omatsuli da aikata laifuffuka akalla 45 wanda su ka hada da sama da fadi, da kuma yin kutun-kutun wajen sace kudi har N3, 645, 000, 000.00.
Hukumar da ke yaki da barayi na EFCC tana zargin Omatsuli da kuma Momoh ne da ba wasu kamfanonin su kwangila domin su karkatar da kudin Gwamnati. Irin wannan danyen aiki dai bai halatta ba a tsarin aikin ofis.
KU KARANTA: EFCC: Malam Mai Rakumi zai sha daurin shekaru 10 a gidan yari
Binciken da Jami’an EFCC su ka gudanar ya nuna cewa tsohon Shugaban Hukumar ta NDDC Injiniya Omatsuli ya rika ba Kamfanin sa na Starline Consultancy Services Limited ayyuka domin awon gaba da makudan kudi na Hukumar.
Wadanda ake tuhuma Injiniya Tuoyo Omatsuli da Francis Momoh sun fadawa Alkali mai shari’a a Kotun da ke Ikoyi watau Salisu Saidu cewa ba su aikata laifuffukan da ake zargin su da aikatawan ba inda su ka kuma nemi a sake su.
Lauyan EFCC Ekene Iheanacho ya nemi a rufe wadanda ake tuhuma a gidan yari domin su rika halartar shari’a. Sai dai Lauyoyin wadanda ake kara sun bayyana cewa ya kamata a bada belin su ne tun da kurkuku sun cika makil.
Yanzu dai Alkali mai shari’a Salisu Saidu ya nemi a cigaba da rike wadanda ake karar a hannun EFCC har zuwa lokacin da Kotu za ta zauna. An dage shari’ar ne zuwa Ranar Juma’a 16 ga Watan nan.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT
Asali: Legit.ng