INEC ta fitar da sunayen 'yan takarar da za su fafata a zaben maye gurbi a jihohin arewa 3

INEC ta fitar da sunayen 'yan takarar da za su fafata a zaben maye gurbi a jihohin arewa 3

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta saki sunayen 'yan takara da jam'iyyun su a zaben maye gurbi na ranar 17 ga wata da za a yi a jihohin Katsina, Bauchi, da Kwara.

INEC ta saki sunayen ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Festus Okoye, kwamishinan hukumar mai kula da bangaren yada labarai da ilimantar da ma su kada kuri'a.

Za a yi zaben maye gurbin ne a mazabar Kankia/Kusada/Ingawa a jihar Katsina, mazabar Toro a jihar Bauchi, mazabar Ekiti/Irepodun/Isin/Oke-Ero a jihar Kwara, da kuma mazabar Ikom II a jihar Kuros Riba.

Zabe maye gurbi a jihohin arewa 3: INEC ta fitar da sunayen 'yan takara da jam'iyyun su

Zabe maye gurbi a jihohin arewa 3: INEC ta fitar da sunayen 'yan takara da jam'iyyun su
Source: UGC

INEC ta bayyana cewar jam'iyyu hudu ne su ka mika sunayen 'yan takarar su daga jihar Katsina.

DUBA WANNA: Wani mutum ya datse kan shugaban matasa a karamar hukumar Oshiomhole

'Yan takara su ne Nasiru Kankia na jam'iyyar PRP, Abdullahi Umar na jam'iyyar YES, Abdulsamad Abdullahi na jam'iyyar PDP, da Abubakar Kusada na jam'iyyar APC.

A mazabar Toro ta jihar Bauchi akwai; Shehu Umar na jam'iyyar PDP da Yusuf Nuhu na jam'iyyar APC.

Daga mazabar Ekiti Irepodun/ Isin /Oke-Ero a jihar Kwara akwai Femi Ara na jam'iyyar LP, Olaniyan Ayorinde, na jam'iyyar UPN, Jimoh Damilare na PDP da kuma Ajayi Bidemi na APC.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel