Yakin duniya na II: Yariman Ingila ya karrama sojojin Najeriya da suka kwanta dama, hotuna

Yakin duniya na II: Yariman Ingila ya karrama sojojin Najeriya da suka kwanta dama, hotuna

- A cigaba da ziyarar da ya ke yi a Najeriya, yarima Charles, mai jiran gadon sarautar kasar Ingila ya ziyarci makarabartar sojoji da ke Abuja

- Yarima Charles ya ziyarci makarabartar ne domin karrama sojojin Najeriya da su ka fafata a yakin duniya na II

- A ranar Talata ne yarima Charles ya iso Najeriya a wata ziyarar wasu kasashen Afrika da ya ke yi tare da matar sa

A yau, Alhamis, ne yariman kasar Wales, Charles George, mai jiran gadon sarautar kasar Ingila ya ziyarci makarabartar sojoji da ke Abuja.

Yarima Charles ya ziyarci makarabartar ne domin karrama dakarun sojin Najeriya da su ka kwanta yayin gwabzawa a yakin duniya na II.

Yarima Charles ya samu rakiyar manyan jami'an hukumar sojin Najeriya.

Yakin duniya na II: Yariman Ingila ya karrama sojojin Najeriya da suka kwanta dama, hotuna

Yariman Ingila ya karrama sojojin Najeriya da suka kwanta dama
Source: UGC

Yakin duniya na II: Yariman Ingila ya karrama sojojin Najeriya da suka kwanta dama, hotuna

Yariman Ingila ya karrama sojojin Najeriya da suka kwanta dama
Source: Twitter

Yakin duniya na II: Yariman Ingila ya karrama sojojin Najeriya da suka kwanta dama, hotuna

Yariman Ingila ya karrama sojojin Najeriya da suka kwanta dama
Source: Twitter

Ko a jiya, sai da yarima Charles ya gana da manyan sarakunan Najeriya, inda aka jiyo sarkin Benin, Ewuare II, na mika bukata ga yariman da ya saka baki domin ganin kasar Ingila ta dawowa da masarautar sa kayan tarihin da ta kwasa a shekarar 1857.

Sarkin ya bayyana cewar dawo ma sa da kayan tarihin zai bashi damar gina gidan tarihi da zai bunkasa tarihi da yawon bude ido a birnin Benin, jihar Edo.

DUBA WANNAN: Wani mutum ya datse kan shugaban matasa a karamar hukumar Oshiomhole

Ewure II na wadannan kalamai ne a cikin wani jawabi da ya gabatar yayin ganawa da yarima mai jiran gadon sarautar kasar Ingila a wani taro da su ka yi jiya a gidan jakadancin kasar Ingila da ke unguwar Maitama a Abuja.

Ragowar sarakunan gargajiya da su ka halarci taron sun hada da Sarkin kasar Ife, Enitan Ogunwusi; Sarkin Musulmi, Sa'ad Abubakar; Sarkin Onitsha, Igwe Alfred; Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, da sauran su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel