Siyasar Kano: Takai ya samu tikitin takarar Gwamna a PRP

Siyasar Kano: Takai ya samu tikitin takarar Gwamna a PRP

Mun samu labari cewa Malam Salihu Sagir Takai wanda ya fice daga Jam’iyyar PDP kwanan nan ya koma Jam’iyyar PRP ya samu tikitin takarar kujerar Gwamna a Jam’iyyar a zaben da za ayi a 2019.

Siyasar Kano: Takai ya samu tikitin takarar Gwamna a PRP

Salihu Takai zai rikewa PRP tuta a Kano a zaben 2019
Source: Facebook

Jam’iyyar adawa ta PRP ta ba Salihu Takai tutar takarar Gwamna na Jihar Kano a zaben 2019 bayan an janye sunan ‘Dan takarar da aka tsaida a baya. A baya dai PRP ta tsaida Sammani Shariff Bashir ne a matsayin ‘Dan takarar ta a 2019.

Ganin cewa lokacin gudanar da zaben fitar da gwani ya kure, shiyasa Jam’iyyar adawar ta PRP ta sauya sunan wanda zai yi mata takarar Gwamna a Jihar Kano. Yanzu dai tuni Jam’iyyar ta sanar da Hukumar INEC wannan canji da aka samu.

Shugaban Jam’iyyar watau Sammani Sharrif Bashir wanda shi ya lashe tikitin takarar Gwamna a kwanaki ya hakura an janye sunan sa daga takarar inda ya amince a maye gurbin na sa da Salihu Takai wanda ya sauya-sheka kwanaki.

KU KARANTA: PRP ta fara janyewa Kwankwasiyya da PDP Mabiya a Jihar Kano

Idan ba ku manta ba Takai ya tsere daga Jam’iyyar PDP ne bayan ya rasa tutar Jam’iyyar a hannun Abba Yusuf wanda Suruki yake wajen tsohon Gwamna Rabiu Kwankwaso kuma Jagoran Darikar siyasar Kwankwasiyya a Jihar ta Kano.

Takai ya doke mutane 8 ne ya samu tikitin takarar Gwamnan a PRP. Daga cikin wadanda su ka nemi takarar akwai tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Kano wanda yayi murabus Farfesa Hafiz Abubakar da kuma Sanata Isa Yahaya Zarewa.

Sauran masu harin kujerar Gwamna a PRP bayan Sammani Sherrif ya janye sun hada da: Janar Sulaiman Wali (Rtd), Alhaji Kabiru Muhammad Gwangwazo, da kuma Alhaji Aminu Baba Nabegu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel