Gwamnatin tarayya na ciyar da yara 'yan makaranta da kwai miliyan 6m da shanu 594 duk sati
Uwargida Maryam Uwais, mai bawa shugaban kasa shawara a kan tsare-tsaren gwamnatin tarayya na tallafawa 'yan kasa, ta bayyana cewar gwamnati na ciyar da yara 'yan makaranta da kwai miliyan 6m da shanu 594 a kowanne mako.
Maryam na bayyana hakan ne a yau, Litinin, yayin karbar bakuncin wakilan gwamnatin kasar Janhuriyar Dimokradiyyar Kongo da su ka zo Najeriya domin kwaikwayon tsarin ciyar da yara a makarantun firamare na gwamnati.
Ta kara da cewa kimanin yara miliyan 9 ne ke amfana daga shirin gwamnatin tarayya na ciyar da yara 'yan makaranta a jihohi 26, tare da sanar da cewar gwamnati na yin hakan ne domin cusa kaunar zuwa makaranta a zukatan yara.
Kazalika ta bayyana cewar shirin ciyarwar ya kara bunkasa harkar noma da kiwo da kuma ta hanyar kulla cinikayya tsakanin 'yan kwangilar gwamnati da manoma.

Asali: Twitter
"A yanzu kowanne dalibi na samun damar cin kwai guda a kowacce rana, idan aka tattara alkaluma zai bayar da adadin kwai miliyan 6.8m duk sati, a iya jihohi 26.
"Yanzu masu kiwon kaji ba su da matsalar sayar da kwai saboda a kowanne abinci da a bawa dalibi daya sai an saka masa kwai guda.
DUBA WANNAN: Likita ya fadi matacce bayan yiwa mutane hudu tiyata a jere
"Muna yanka shanu 594 kowanne sati bayan tan din kifi 83 da ake amfani da shi wajen ciyar da yaran," a kalaman uwargida Maryam.
A nasa jawabin, jagoran tawagar wakilan kasar DRC, Mista John Mugabushaka, ya bayyana cewar gwamnatin kasar su ce ta aiko su domin kawai su samu bayanai a kan yadda Najeriya ke gudanar da tsarin ciyar da dalibai da gwamnatin kasar ta DRC ke burin farawa.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng