Ba kan mu farau ba: Oshiomhole ya ba Surukin sa kujerar Majalisa – Nwosu

Ba kan mu farau ba: Oshiomhole ya ba Surukin sa kujerar Majalisa – Nwosu

Mun ji cewa Uche Nwosu wanda shi ne Surukin Gwamna Rochas Okorocha kuma wanda yake da burin cin gadon kujerar Gwamnan na Jihar Imo ya soki Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Adams Oshiomhole.

Ba kan mu farau ba: Oshiomhole ya ba Surukin sa kujerar Majalisa – Nwosu
Uche Nwosu yace har gobe shi ne ainihin 'Dan takarar APC a Imo
Asali: UGC

Mista Uche Nwosu yayi jawabi kwanan nan bayan Majalisar NWC ta Jam’iyyar APC mai mulki ta cire sunan sa daga matsayin ‘Dan takarar Gwamna inda ta zabi Sanata Hope Uzodinma ya rike mata tuta a zaben Gwamnan Jihar Imo 2019.

Nwosu ya bayyana cewa Adams Oshiomhole yana adawa da takarar sa ne saboda Surukin sa Gwamna Okorocha ya samu takarar Sanatan Imo ta Yamma. Sai dai Nwosu yace ba a kan sa aka fara kakaba Suruki ya samu wata kujera ba.

‘Dan takarar Gwamnan da Okorocha ya tsaida yayi ban-bami inda bayyana cewa Shugaban na APC na kasa Adams Oshiomhole shi ma ya ba Surukin sa tikitin Majalisa a Jihar Edo kuma har gobe bai ajiye mukamin sa a dalilin hakan ba

KU KARANTA: Okorocha da Amosun abin kunya ne ga jam'iyyar APC - Oshiomhole

Mista Nwosu ya fadawa ‘Yan jarida a Garin Owerri cewa Adams Oshiomhole ya ba su kunya kwarai da wannan danyen aiki da yayi. Nwosu yace sn kasance a da su na koyi da Shugaban na APC kafin yayi wannan baram-barama a Jihar Imo.

Uche Nwosu yace Oshiomhole bai duba darajar tsufan domin haka nan yake sakin baki yana magana. Mai neman kujerar na Gwamna ya kara da cewa abin kunya ne ace mutum irin Adams Oshiomhole ne Shugaban Jam’iyyar APC na kasa.

Har yanzu dai ‘Dan takarar yace babu wanda ya isa ya hana sa tikitin sa ba don haka yace shi ne ainihin wanda zai rikewa APC tuta a Jihar Imo a zaben 2019 kuma yace ba zai bar APC ya koma wata Jam’iyya ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng