Magoya bayan Kwankwaso 5000 sun sauya sheka zuwa APC a jihar Kebbi
Da sanadin shafin jaridar The Punch mun samu rahoton cewa, kimanin mambobi 5000 'yan kungiyar nan ta Kwankwasiyya suka sauya sheka daga jam'iyyar adawa ta PDP zuwa APC a jihar Kebbi dake Arewa maso Yammacin Najeriya.
Mataimakin gwamnan jihar, Alhaji Sama'aila Yombe, shine ya yiwa wannan mambobi lale maraba yayin sauyin shekarsu a shelkwatar jam'iyyar dake Birnin Kebbi a yau Talata.
Jagoran wannan kungiya ta magoya bayan Kwankwasiyya yayin sauyin shekar su, Abdullahi Nayalwa ya bayyana cewa, sun yanke wannan shawara ne a sakamakon kwazon gami da hobbasan shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma gwamnan jihar Abubakar Atiku Bagudu, musamman akan harkokin noma.
Yayin karbarsu hannu biyu-biyu, Yombe ya yabawa wannan gagarumar shawara da suka yanke tare da bayar da tabbacinsa a gare su wajen ba su duk wata kulawa da kwararar duk wani romo na jam'iyyar a gare su cikin adalci.
KARANTA KUMA: Najeriya da kasashe 69 za su halarci taron Ilimi a Kasar India
Jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, Kwankwasiyya wata kungiyar siyasa ce bisa jagorancin tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, daya daga cikin manema tikitin takarar kujerar shugaban kasa a jam'iyyar PDP da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya lashe yayin zaben fidda gwani da aka gudanar makonni kadan da suka gabata.
Kazalika jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, wani Malalacin Direban ya shiga hannun hukumar 'yan sanda da laifin lalata da karamar yarinya 'yar shekara biyu a jihar Legas.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng