Uwargidar Buratai ta yi ma wasu al’ummar jahar Taraba sha tara ta arziki
Uwargidar babban hafsan rundunar Sojan kasa, Laftanar janar Tukur Yusuf Buratai, Ummu Kulsum Buratai ta kaddamar da wasu rukunin azuzuwa da kuma dakin gwaje gwajen kimiyya na zamani da ta gina ma makarantar sakandari dake garin Mutum Biyu na jahar Taraba.
Rahoton kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta ruwaito rukunin azuzuwan guda uku na dauke da jimillan azuzuwa guda ashirin da hudu ne, sai kuma famfon tuka tuka mai amfani da hasken rana guda biyu, da kuma dakin gwaje gwaje dake dauke da kayan aiki irin na zamani.
KU KARANTA: Real Madrid ta sanar da sabon mai horas da yan wasa, karanta abubuwa 10 game da shi
Hajiya Ummu Kulsum, wanda ita ce shugaban matan hafsoshin rundunar sojan kasa, NAOWA ta bayyana cewa ta dauki gabarar gudanar da wannan muhimmin aiki ne a matsayinta na cikakkiyar yar garin mutum biyu, kuma wanda take kishin asalinta.
Dayake bata samu daman halartar taron ba, amma ta samu wakilcin Hajiya Rabi Mohammed, uwargidar kwamandan bataliya ta 20 dake garin Serti na jahar Taraba, wanda ta bayyana ta yi dauki nauyin aikin ne sakamakon burinta na ganin ta samar da ingantaccen ilimi.
“Na mayar da hankalina ga ayyukan kiwon lafiya da ilimi ne saboda sune ginshikai guda biyu mafi muhimmanci ta wajen samar da cigaba mai daurewa a tsakanin kowanne al’umma.
“Ruwa shine rayuwa, lafiya kuma jari ne, ilimi kuma shine babban makamin da mutum zai iya amfani da shi wajen kawo sauyi mai inganci a Duniya.” Inji ta.
Haka zalika Ummu ta yi kira ga matasan yankin da su guji ta’ammali da miyagun kwayoyo da zinace zinace, inda ya bukacesu dasu rungumi zaman lafiya da juna, ta haka ne kadai zasu samar da kyakkyawan cigaba mai daurewa.
A nasa jawabin, shugaban karamar hukumar Gassol, Alhaji Yahuza Yaya’u ya bayyana godiyarsa ga uwargidar babban hafsan rundunar sojin kasa, Ummukulsum Buratai, inda yace ya gudanar da ayyuka masu muhimmanci da dama don amfanin matasan yankin.
Daga karshe yayi kira ga sauran yayan garin mutum biyu da Allah ya daukakasu da suyi koyi da Hajiya Ummukulsum wajen samar da ayyukan da zasu kyautata rayuwr al’ummar garin gaba daya.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng