Takardun shaidar karatun Buhari sun bace bat! – Fadar shugaban kasa

Takardun shaidar karatun Buhari sun bace bat! – Fadar shugaban kasa

Fadar shugabann kasa ta bayyana cewa rundunar Sojin Najeriya ta tabbatar da takardun makarantar shugaban kasa Muhammadu Buhari sun bace bat! Kamar yadda kaakakin shugaban kasa, Femi Adesina ya bayyana, inji rahoton The Cables.

Majiya LEGIT.com ta ruwaito Adesina ya bayyana haka cikin wata hira da aka yi da shi da jaridar The Nation, inda yace maganar ta mutu, an wuce wajen, kuma duka masu tayar da maganar marasa aikin yi ne.

KU KARANTA: Wani dan majalisan PDP ya tsallake rijiya da baya yayin da yan bindiga suka bude masa wuta

Idan za’a tuna shugaba Buhari bai mika takardunsa dake nuna shaidar cewa ya kammala karatun sakandari ba, wanda kuma shine karancin matakin karatun da dokokokin Najeriya suka amince dan takara ya taka kafin ya taka takarar shugaban kasa.

Don haka ne wannan lamari ya tayar da kura matukar gaske a dandalin siyasar Najeriya, inda wasu suka tubure lallai sai Buhari ya bayyana takardunsa, amma Adesina ya mayar musu da martani, inda yake cewa:

“Maganar takardun karatun Buhari ya wuce, marasa aikin yi ne akwa ke cigaba da rurutata, tun kafin zaben shekarar 2015 aka kashe maganar, ina ganin masu tayar da maganar nan sun fahimci zasu sha kayi a zaben 2019 ne, don haka suke neman tudun dafawa

“A lokacin da Buhari da sa’anninsa suka shiga aikin Soja, sai aka amshe musu takardunsu na asali, hatta tsohon shugaban hafsan hafsoshin Sojan Najeriya, Alani Akinrinade ya tabbatar da batun amshe takardun nasu, don haka hukumar Soji ta san inda takardun suke.

“Amma hukumar tace ta batar da takardun, don haka, haka baya nufin Buhari ba yi makaranta ba, tun da har ya zana jarabawar kammala sakandari, kuma ya ci, sa’annan ya halarci horo daban daban, hatta kwalejin yaki na Birtaniya ya je.” Inji shi.

Daga karshe Kaakakin ya akwai wadanda suke ganin Buhari bai je makaranta ba, har ma suka garzaya gaban Kotu, kuma kotu ta bayyana cewa basu da gaskiya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng