Buhari da shugaba Talon na kasar Benin sun kaddamar da aikin hadin gwuiwa a Seme, hotuna
A jiya, Talata, ne Najeriya da kasar Benin su ka kara karfafa dangantakar da ke tsakanin ta hanyar bude wata sabuwar iyaka ta hadin gwuiwa tsakanin kasashen biyu a karkashin hurumin kungiyar kasashen Afrika (ECOWAS).
Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewar an fara aikin gina iyakar ne da ke Seme-Krake a Badagry ta jihar Legas a shekarar 2011.
Kungiyar kasashen Turai (EU) ce ta dauki nauyin gina ofishin iyakar da ya lashe a kalla Yuro miliyan€18.2 tun farkon fara shi da kammalawa.
Da yake jawabi yayin bude ofishin, shugaban kungiyar kasashen Afrika ta yamma, Muhammadu Buhari, ya mika godiya ta musamman ta EU bisa kokarinta na gina yankin Afrika ta yamma.
Buhari ya bayyana cewar bayan daukan nauyin gina ofishin iyakar Najeriya da Benin, EU ta daukin nauyin gina ofishin iyakar kasashen Ghana da Togo da ke Noepe-Akanu da kuma tsakanin kasar Benin da janhuriyar Nijar.
DUBA WANNAN: Abinda zamu yi domin kara inganta rayuwar 'yan Najeriya - Buhari
Iyakar Seme-Krake da ke na daga cikin manyan iyakoki da 'yan kasashen Afrika ke amfani da ita domin zirga-zirgar mutane da jigilar kaya.
A nasa bangaren, shugaba Patrice Talon na kasar Benin, ya ce Najeriya da Benin na da tsohon tarihi ta fuskar kyakykyawar dangantaka tare da bayyana cewar kaddamar da ofishin iyakar zai kara dinke kasashen biyu.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng