Sarki Sanusi ya nada sabon dan masanin Kano, hotuna

Sarki Sanusi ya nada sabon dan masanin Kano, hotuna

A yau ne, sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, ya nada Alhaji Abdulkadir Maitama Sule, a matsayin sabon dan masanin Kano.

An nada Abdulkadir, da ga marigayi tsohon dan masanin Kano, Sule Maitama, yau, Asabar, a fadar sarki Sanusi II dake garin Kano.

A ranar 2 ga watan Yuli na shekarar 2017 ne Allah ya yiwa dan masanin Kano, Maitama Sule, rasuwa a wani asibitin kasar Masar (Egypt) bayan ya sha fama da cutar numoniya da ciwon kirji.

Kafin rasuwar sa, Maitama Sule, ya kasance dan siyasa da ya taba rike mukamin bulaliyar majalisar wakilai a tsakanin shekarar 1955 zuwa 1956.

Sarki Sanusi ya nada sabon dan masanin Kano, hotuna

Alhaji Abdulkadir sabon dan masanin Kano
Source: Twitter

Sarki Sanusi ya nada sabon dan masanin Kano, hotuna

Nadin sabon dan masanin Kano
Source: Twitter

Sarki Sanusi ya nada sabon dan masanin Kano, hotuna

Sabon dan masanin Kano
Source: Twitter

An haifi marigayi Maitama a Shekarar 1929, a unguwar Yola, cikin garin Kano. Maitama shi ne na uku a jirin 'ya'yan gidansu, ragowar su ne Rabi, wacce ake kira Yaya ta Zagi da Maimuna wacce ake kira Yaya ta Bichi.

An sa masa suna Yusuf, saboda sunan Mahaifin Madakin Kano Mahmudu, shi Madaki yana kiran shi Abbana. Sunan Maitama kuwa an sa masa shi ne saboda Galadiman Kano Yusuf, saboda an yi amfani da makamai sosai lokacin basasar Kano. Akan yi wa duk wani mai suna Yusuf lakabin Maitama.

DUBA WANNAN: Hadimar Buhari ta farkewa shugaban CAN laya a kan sukar shugaban kasa

Madakin Kano ya kasance hadimin Mahaifin Maitama, Abba Sule Danmuri, mai kula da dukkan al'amuransa na gida da kula da Dawakai.

Maitama na dan shekaru 4 mahaifiyarsa Hauwa, wacce ake kira 'Yarkayi ta rasu. Ita Allah ya yi ta ne mace mai ban dariya, mai raha, ba ta fushi, shi ya sa duk bikin da ya tashi ita ake kira ta yi ta magana a gidan biki, halinta da iya maganarta Maitama ya gado.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel