Mayakan Boko Haram sun kaiwa sojojin Najeriya harin bazata

Mayakan Boko Haram sun kaiwa sojojin Najeriya harin bazata

A jiya, juma'a, 12 ga watan Oktoba, ne da misalin karfe 5 na yamma, mayakan kungiyar Boko Haram suka kaiwa dakarun sojin Najeriya, runduna ta 118 harin bazata.

A sanarwar da hukumar sojin ta fitar a shafinta na Tuwita, ta bayyana cewar mayakan kungiyar ta Boko Haram sun kai harin ne a sansanin sojojin da ke Arege a karamar hukumar Mobarr dake jihar Borno.

Sai dai jaruman dakarun sojin sun yi nasarar dakile harin tare da mayar da kaikayi kan mashekiya.

Bayan sojojin sun dakile harin, sun yi nasarar kwace wasu makamai daga wurin 'yan ta'addar da su ka hada da wata motar dakon bindiga tare da lalata wasu motocin biyu. Yanzu haka dakarun sojin na cigaba da farautar mayakan kungiyar Boko Haram da su ka tsere bayan kai harin.

Mayakan Boko Haram sun kaiwa sojojin Najeriya harin bazata
sojojin Najeriya
Asali: Facebook

Ko a ranar Alhamis da ta gabata, Legit.ng ta kawo maku labarin cewar dakarun rundunar sojin Najeriya, bataliya ta 112, dake aikin tabbatar da da zaman lafiya a jihar Borno, sun kashe mayakan kungiyar Boko Haram masu yawa a ranar, Alhamis, 11 ga watan Oktoba, 2018.

DUBA WANNAN: Fallasa: Hadimar Buhari ta farkew shugaban CAN laya a kan yawan sukar shugaban kasa

A wata sanarwa da hukumar sojin Najeriya ta fitar a daren na ranar Alhamis, ta bayyana cewar dakarun sojin sun kashe mayakan kungiyar Boko Haram din ne a wani faturu da suka gudanar a tsakanin kwanar Bale da Ajiri da ke jihar ta Borno. Sojojin sun kai samame yankin ne bayan tabbatar da cewar mayakan kungiyar Boko Haram din na amfani da wurin domin buya duk lokacin da jami'an soji ke farautar su.

Shugaban rundunar sojin, Laftanal janar Tukur Yusuf Buratai, ya yabawa kwazon sojojin tare da basu umarnin su kara matsa wa da sintiri a yankin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng