Zan yi sakayya mai kyawu ga wadanda suka nemi tikitin takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP - Atiku
Tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar, ya sha alwashi tare da lasar takobbi kan cewa zai yi sakayya mai kyawun gaske ga sauran jiga-jigan kasar nan 11 da suka nemi tikitin takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP tare da shi.
Atiku wanda shine ya lashe tikitin takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP yayin zaben fidda gwani da aka gudanar a karshen makon da ya gabata, ya sha alwashi na kyakkyawar sakayya ga sauran abokanan takararsa muddin ya zamto shugaban kasar nan a yayin babban zabe na 2019.
Kamar yadda shafin jaridar Vanguard ta ruwaito, Atiku ya bayyana hakan ne cikin babban birnin kasar nan na tarayya yayin ganawa da amintattun mambobin jam'iyyar PDP, inda ya nemi su hada kai wajen goyon bayan sa kan kudirin inganta jin dadi na rayuwar al'ummar Najeriya.
A cewar sa, hadin kan da manema takarar tikitin suka gudanar yayin zaben fidda gwanin takara da aka gudanar can birnin Fatakwal na jihar Ribas ya tabbatar da cewa, jam'iyyar ta shirya tsaf domin ganin ta fatattki APC daga fadar shugaban kasa a zaben 2019.
KARANTA KUMA: 2019: Muna bayan Shugaba Buhari - 'Kungiyar Karnukan Motocin haya ta Najeriya
Yayin jawaban shugaban kungiyar amintattu na jam'iyyar, Sanata Wada Jibrin, ya taya Atiku murna tare da fadakar da shi akan neman goyon bayan sauran abokanan takararsa domin hada gwiwa da juna ta tabbatar da nasarar jam'iyyar yayin zaben 2019 da hausawa kan ce hannu da yawa maganin kazamar miya.
Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, daya daga cikin wadanda suka nemi takarar tikitin jam'iyyar, Ibrahim Dankwabo ya taya Atiku murna tare da shan alwashin goyon bayan sa 100 bisa 100 domin tabbatuwar nasarar jam'iyyar yayin babban zabe na kasa da za a gudanar a badi.
Na nan tafe, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika muna mika godiyar mu ta musamman a gare ku yayin da kuke ci gaba da kasancewa tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng