Tuwona maina: Jam’iyyar APC ta yi cinye-du a zaben kananan hukumomin jahar Jos

Tuwona maina: Jam’iyyar APC ta yi cinye-du a zaben kananan hukumomin jahar Jos

Jam’iyyar APC mai mulki ta samu gagarumar nasara a zaben shuwagabannin kananan hukumomin jahar Filato daya gudana a ranar Alhamis, 12 ga watan Oktoba, kamar yadda gidan talabijin na Channels ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito shugaban hukumar zabe mai zaman kanta na jahar Filato, Fabian Ntung ne ya bayyana haka a yayin da yake karanto sakamakon zaben gaba daya, inda yace APC ta lashe kafatanin kananan hukumomin jahar goma sha uku.

KU KARANTA: Obasanjo ya bayyana muhimman dalilai 5 da suka say a gafarta ma Atiku gabanin zaben 2019

Sai dai Mista Fabian yace zabe a kananan hukumomin Mangu, da Langtang ta Arewa bai kammalu ba sakamakon barkewar rikici a yayin zaben, da kuma matsaloli da suka dinga tasowa.

Bugu da kari shugaban hukumar zaben ya kara da cewa jam’iyyar APC mai mulki ta lashe zaben kansiloli a mazabu dari biyu da hudu a zaben wanda jam’iyyar adawa ta PDP lashe mazabu shidda kacal.

Sai dai jam’iyyar ta PDP ta yi kakkausan suka ga wannan zabe, inda ta bayyanashi a matsayin fashin da makami da tsakar rana babu kunya babu tsoron Allah, don haka tace bata amince da sakamakon wannan zabe ba.

Shugaban jam’iyyar PDP a jahar Filato, Damishi Sango ne ya tabbatar da rashin amincewar jam’yyar PDP da sakamakon zaben shuwagabannin kananan hukumomin, inda yace har zuwa lokacin tattara rahotonnan akwai akwatunan zaben da basu yi ido hudu da takardun rubuta sakamakon zabe ba.

A wani labarin kuma, dan takarar jam’iyyar PDP na mukamin shugaban kasar Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar ya kai gaisuwa wajen tsohon maigidansa Olusegun Obasanjo, inda ya nemi gafararsa tare da neman goyon bayansa, kuma yayi dace Obasanjon ya gafarta masa tare da alkawarin mara masa baya.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa za ta koma LEGIT.ng Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel