Bidiyon cin hanci: Sarki Muhammadu Sunusi ye nemi a rufa ma Ganduje asiri

Bidiyon cin hanci: Sarki Muhammadu Sunusi ye nemi a rufa ma Ganduje asiri

Mai martaba sarkin Kano, Malam Muhammadu Sunusi II ya hana a yi ma gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje tereren bankada bias bullar wata rahoto daga jaridar Daily Nigerian da ta fallasa gwamnan a cikin bidiyo na musamman yayin da yake karbar cin hancin dala miliyan biyar.

Jaridar Rariya ta ruwaito Sarki Muhammadu Sunusi ya nemi wani gidan rediyo mai zaman kanta a jahar Kano, Freedom Radio da kada su yayata wannan badakala, don zai iya zama cin fuska ga gwamnan.

KU KARANTA: Malaman addinin kirista sun shirya addu’ar kwana 40 don nema ma Buhari nasara a 2019

Bidiyon cin hanci: Sarki Muhammadu Sunusi ye nemi a rufa ma Ganduje asiri
Sarki da Ganduje
Asali: Twitter

Majiyar Legit.ng ta ruwaito mai martaba Sarki yayi haka ne ta hanyar neman alfarmar wani jami’in gidan rediyon dake gabatar da shirin inda ranka, Nasir Salisu Zango, shirin dake bankado badakaloli tare da yayatasu a gidan rediyon Freedom.

Wadanda suka saurari shirin a daren Laraba 10 ga watan Oktoba sun ce Nasiru ya tabo labarin, inda aka jiyo shi yana bayyana gwamnan a matsayin ‘Sahibul fulus, wal dalalliyar amurkiyya’ sai dai kai tsaye bai bayyana sunansa ba, kuma bai yi alkawarin cigaba da rahoton ba.

Sai dai majiyarmu ta ruwaito wata majiya ta karkashin kasa dake cewa; “Mai martaba sarki ne kadai yake da wannan alfarma a duk fadin Kano, sai kuma wasu Malamai da ba za’a rasa ba, amma ko maigidan rediyon Freedom bai isa ya hana Zango daukar labarin ba.” Inji shi.

Shi dai wannan rahoto da ya fara bayyana daga mawallafin jaridar Daily Nigerian, Jaafar Jaafar ta bayyana yadda gwamnan ya karbi cin hancin dala miliyan biyar daga hannun yan kwangila ya zubasu a aljihun rigarsa da na wando, sa’annan ya kara amsan dala miliyan uku a wani wajen ya zuba a babban riga.

A wani labarin kuma wasu kungiyoyin kare hakkin biladama sun bayyana wannan rahoto na karbar cin hanci da rashawa a matsayin wata tuggu da tsohon gwamnan jahar Kano Rabiu Musa Kwankwaso ya shirya ma Ganduje don ya bata masa suna.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa za ta koma LEGIT.ng Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel