Jam'iyyun Siyasa sun yiwa Mata rashin adalci yayin Zabukan Fidda Gwanaye - NCWS

Jam'iyyun Siyasa sun yiwa Mata rashin adalci yayin Zabukan Fidda Gwanaye - NCWS

Wata kungiyar Mata ta NCWS, The National Council of Women Societies, ta zargi mafi akasarin jam'iyyun siyasa na kasar nan da yiwa Mata rashin adalci yayin zabukan fidda gwanayen takara da aka gudanar a kwana-kwanan.

Ko shakka babu jam'iyyu da dama na kasar nan sun gudanar da zabukan fidda gwanayen takara na kujerun siyasa daban-daban makonnin kadan da suka gabata domin daura damara tare da sanya sulke na fafatawa da zama cikin shirin babban zabe na 2019.

A yayin haka kungiyar da sanadin mai jagorancin ta, Misis Gloria Shoda, ta bayyana cewa, rashin adalcin da aka yiwa Mata yayin zabukan fidda gwanaye na jam'iyyu ya kawo nakasun karfin gwiwarsu ta ci gaba da damawa a cikin harkokin siyasa.

Misis Shoda ta bayyana hakan ne yayin ganawa da manema labarai cikin babban birnin kasar na Abuja, inda ta ce tsadar takardun bayyana kudirin takara da kuma dambarwar rikici da tayi kakagida ta sanya suka gaza fitowa kada kuri'un su yayin zabukan fidda gwanaye.

Jam'iyyun Siyasa sun yiwa Mata rashin adalci yayin Zabukan Fidda Gwanaye - NCWS
Jam'iyyun Siyasa sun yiwa Mata rashin adalci yayin Zabukan Fidda Gwanaye - NCWS
Asali: Depositphotos

Legit.ng ta fahimci cewa, mafi akasarin jam'iyyun sun saba alkawurran da suka dauka na tabbatar da gudanar zabe cikin kwanciyar hankali tare da tashin doron Zabuwa na takardun bayyana kudirin takara da ta sanya Mata suka janye jikin su daga harkokin siyasa.

Ko shakka ba bu kungiyar ta bayyana takaicin ta kwarai da aniyya dangane da wannan lamari da kiraye shi a matsayin rashin adalci ga mata kan harkokin siyasa.

KARANTA KUMA: Ambaliyar ruwa ta shafe gonaki 500 na Shinkafa a jihar Bayelsa

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, Uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari, ta bayar da tabbacin ta na goyon bayan Mata manema takarar kujerun siyasa daban-daban a fadin kasar nan.

Uwargidan shugaban kasar ta bayyana hakan ne yayin da Mata sabbin shugabannin jam'iyyar APC reshen dukkanin jihohi 36 na fadin kasar nan suka ziyarce ta a fadar shugaban kasa dake babban birnin na tarayya.

Kazalika jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, uwargidan shugaban kasar ta jaddada matsayarta kan cewa Mata suke taka muhimmiyar rawar gani wajen nasarorin da aka samu yayin duk wani zabe na kasar nan.

Na nan tafe, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika muna mika godiyar mu ta musamman a gare ku yayin da kuke ci gaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel