Sarkin Kano ya bayyana dalilin samun koma bayan ilimi a Najeriya, ya kawo mafita

Sarkin Kano ya bayyana dalilin samun koma bayan ilimi a Najeriya, ya kawo mafita

- Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya shawarci gwamnatin tarayya ta kafa dokar fara koyar da darussa cikin harsunan Najeriya

- Muhammadu Sanus II ya ce harshen turanci na da amfani amma koyar da dalibai da harsunan iyayensu zai karawa daliban fahimta da hazaka

- Sarkin har ila yau ya shawarci gwamnatin tarayya da kara kason da ta ke warewa fanin Ilmi a kasafin kudin kasa

A yau Laraba ne Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya shawarci gwamnatin tarayya ta yiwa tsarin Ilimin Najeriya garambawul yadda za a rika koyar da darrusa da harsunan Najeriya a maimakon amfani da turanci kawai.

Sarki Sanusi ya bayar da wannan shawarar ne a wata taron Shugabanin Sarakunan Gargajiya na Arewacin Najeriya da aka shirya a Kaduna. Ya ce amfani da turanci zalla wajen koyar da darrusa a makarantu yana daga cikin dalilin da yasa dalibai basu fahimtar karatun da ake koyar da su.

Sarki Sanusi ya bayar da muhimmiyar shawara domin inganta ilimi a Najeriya
Sarki Sanusi ya bayar da muhimmiyar shawara domin inganta ilimi a Najeriya
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Majalisa ta nada sabon mataimakin shugaban masu rinjaye

Ma'aikatar Ilimi na Tarayya, Hukumar Samar da Ilimin Frimare, Cibiyar Ilmantar da A'lumma, Gidauniyar Sultan na zaman lafiya da cigaba da Hukumar UNICEF ne su kayi hadin gwiwa wajen shirya taron.

A cewarsa, Turanci yana da muhimmanci amma ba a bukatar turanci kafin mutum ya zama likita ko Injiniya da duk wani abin da mutum ya ke son zama.

Ya jadada cewar fara koyar da dalibai da harsunan iyayensu zai taimaka matuka wajen kara musu fahimta da hazaka wajen karatu da kuma amfani da abubuwan da suka koya domin inganta rayuwarsu da ta al'umma baki daya.

Sanusi ya kuma koka kan yadda gwamnatin tarayya ke bawa sashin ilimi kaso mara tsoka na 7% a maimakon 26% kamar yadda ya dace.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164