Siyasar 2019: Wani Malamin addini ya dukufa saukar Qur’ani a kullum don samun nasarar Atiku

Siyasar 2019: Wani Malamin addini ya dukufa saukar Qur’ani a kullum don samun nasarar Atiku

Karakara kaka, a yayin da jam’iyyu suka kammal fitar da yan takarkarunsu na mukaman siyasa daban daban, gami da cigaba da karatowar babban zaben 2019, tuni jama’a masoya da magauta suka fara kullen ganin nasu ya samu nasara ko karya abokin hamayyarsu.

Zuwa yanzu dai kowa ya sani cewa jam’iyyar APC mai mulki ta sahhale ma shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya yi tazarce, yayin da jam’iyyar adawa ta PDP ta tsayar da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar a matsayin nata dan takarar.

KU KARANTA: KananaN yara 59, 000 ne ke rasa rayukansu a sanadiyyar amai da zawo a Najeriya

Daga cikin kokarin da masoya ke yi na ganin dan takararsu ya kai bantensa, akwai wani matashin Malami daga garin Zaria mai suna Hibban Sunusi, wanda Allah ya jarabceshi da kaunar Atiku Abubakar, wanda hakan ya sa shi daukan wani babban alkawari game da takarar Atikun.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Malam Hibban ya dauki alwashin saukan karatun Al-Qur’ani a kowanne ranar duniy har ranar da za’a kada kuri’un a takarar shugaban kasa, dun don ganin Atiku Abubakar ya samu nasara a wannan zabe tare da cika burinsa na zama shugaban kasar Najeriya.

Siyasar 2019: Wani Malamin addini ya dukufa saukar Qur’ani a kullum don samun nasarar Atiku
Malamai
Asali: Facebook

A yanzu haka wannan matashi ya fara sauke wannan nauyi daya daukan ma kansa, inda aka hangeshi yana karatun Al’-Qur’ani mai tsarki tare da sauran malamai a gidansu dake unguwar Hanwa Rinji cikin garin Zaria.

A wani labarin kuma an samu wani matashi da ya fito daga garin Zaria da nufin isa babban birnin tarayya Abuja a kasa don bayyana tsananin soyayyar da goyon bayan da yake yi ma dan takarar shugaban kasa a inuwar jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar.

Wannan matashi mai suna Kamaluddeen Bashir yace yana sa ran zai isa Abuja cikin kwanaki biyar, inda ya kwashe kwana daya daga Zaria zuwa garin Kaduna, sai dai matashin yace an yi masa fashin guzurinsa a tsakanin Zaria zuwa Kaduna.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa za ta koma LEGIT.ng Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel