Da dumi dumi: Hukumar zabe ta haramta ma jam’iyyar APC fitar da yan takarkaru a Zamfara

Da dumi dumi: Hukumar zabe ta haramta ma jam’iyyar APC fitar da yan takarkaru a Zamfara

Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta, INEC ta sanar da uwar jam’iyya APC ta kasa cewa ta haramta mata fitar da yan takarkarun mukamai daban daban a jahar Zamfara, don haka jam’iyyar ba za ta fafata a babban zaben shekarar 2019 ba.

Jaridar Premium Times ta ruwaito INEC ta yanke wannan hukunci ne duba da gazawar jam’iyyar APC a wejen mika mata sunayen yan takarkarunta daga jahar Zamfara har zuwa ranar 7 ga watan Oktoba, ranar da hukumar ta kulle amsan sunayen yan takara.

KU KARANTA: Wata yar Najeriya ta halaka kanta bayan gwamnatin kasar Ghana ta garkame mata shago

INEC ta sanar da shugaban jam’iyyar APC, Adams Oshimole wannan mataki da ta dauka a hukumance a cikin wata wasika da ta aika masa a ranar Talata 9 ga watan Oktoba, kamar yadda majiyar Legit.ng ta gano.

Zaben fidda na gwani na jam’iyyar APC a jahar Zamfara bai yiwu ba sakamakon bakar adawa dake tsakanin bangarori biyu masu karfi a jam’iyyar jahar, bangarorin kuwa sune na gwamnan jahar Abdul Aziz Yari da bangaren yan takarar gwamnan jahar su takwas a karkashin jagorancin Sanata Kabiru Marafa.

A yayin da Gwamna Yari ke kokarin ganin ya tabbatar da kwamishinan kudi, Mukhtar Idris a matsayin wanda zai gaje shi, shi kuwa Kabir Marafa na ganin wannan buri ba gwamnan a matsayin dauki daura, wanda ba zai lamunta ba.

Sakamakon wannan rikita rikitan da ya dabaibaye zaben an samu akalla mutane biyar da suka rasa rayukansu a jahar Zamfara, yayin da mutane da dama suka samu rauni daban daban, hakan ne ya sanya uwar jam’iyyar APC ta kasa ta rusa shugabancin APC na jahar gaba daya.

Sai dai wannan hukunci na hukumar zabe ya nuna jam’iyyar PDP za ta tsinci dami a kala kenan a zaben 2019 idan har hukuncin bai sauya ba, inda za ta fafata ita kadai ba tare da wata babbar jam’iyyar hamayya mai karfi ba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa za ta koma LEGIT.ng Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel