Bayan ganawa da Obasanjo, Afenifere ta fadi dan takarar da zata goyawa baya
Hadaddiyar kungiyar kabilar Yoruba, Afenifere, ta yi wata ganawa da tsohon shugaban kasa Obasanjo a gidansa dake Abeokuta, jihar Ogun, domin tattauna zaben shekarar 2019.
Bayan kammala taron na tsawon fiye da sa'o'i biyu, kakakin kungiyar, Yinka Odumakin, ya shaidawa manema labarai cewar sun tattauna batun dan takarar da zasu goyawa baya ne a zaben shekarar 2019.
Ya bayyana cewar kungiyar, ko kadan ba ta cikin shakku a kan dan takarar da ya dace ta goyawa baya saboda abu ma fi muhimmanci a wurinsu shine batun sake fasalin kasa.
Wadannan kalamai na Odumakin daidai su ke da bayyana cewar kungiyar Afenifere na goyon bayan takarar Atiku Abubakar, saboda shi ne ke yakin neman zabe da maganar canja fasalin kasa.
Odumakin ya kara da cewar, "a kwanakin baya, tsohon shugaban kasa Obasanjo ya ziyarci dattijo Ayo Adebanjo a jihar Legas, wannan ziyara ce ta godiya gare shi da kuma daukan matsaya dangane da dan takarar da kabilar Yoruba zata goyawa baya a zaben 2019.
DUBA WANNAN: APC: Mata biyu sun bayar da mamaki a jihar Adamawa, sun lashe takarar kujerar Sanata
Da yake karin bayani a kan ganawar ta su, Odumakin ya ce dole su goyi bayan duk dan takarar da zai canja fasalin Najeriya domin ba zata cigaba ba idan har ba garambawul aka yi mata ba.
A wani labarin na Legit.ng, kun ji cewar a yayin da hukumar zabe ta tsayar da gobe, Laraba, a matsayin ranar karshe ta karbar sunayen 'yan takara, zababben dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, zai zabo abokin takararsa daga yankin kudu maso yama na 'yan kabilar Yoruba.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng