Dambe: Sanata Kabiru Marafa ya musanta kama shi da aka ce DSS sun yi

Dambe: Sanata Kabiru Marafa ya musanta kama shi da aka ce DSS sun yi

Wakilin al’ummar Zamfara ta tsakiya a majalisar dattawan Najeriya, kuma shugaban kwamitin man fetir na majalisar, Sanata Kabiru Marafa ya musanta rahotannin dake yawo a kafafen sadarwar zamani na cewa wai jami’an hukumar DSS sun yi ram da shi.

Marafa ya musanta wannan rahoto dake cewa wai dambe ya kaure tsakaninsa da wasu yan takarar gwamnan jahar Zamfara a karkashin inuwar jam’iyyar APC, daga nan ne jami’an DSS dake wajen suka kama shi, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

KU KARANTA: Turnuku: Dakarun Sojin Najeriya sun yi gaba da gaba da mayakan Boko Haram a Borno

Da yake jawabi ta bakin kaakakinsa Abubakar Umar, Marafa ya bayyana cewa gwamnan jahar Zamfara, Abdul Aziz Yari ne ya shirya wannan labari tare da watsa shi ta hannun yan barandansa.

“An janyo hankalina ga wasu rahotanni dake yawo a kafafen sadarwar na cewa wai jami’an DSS sun kamani, wannan ba wani abu bane illa karirayin da wasu mutane mashaya jini suke yadawa game da ni, suna aikata haka ne don ganin sun sauya burin mutanen Zamfara.

“A matsayina na dan majalisa, zan cigaba da gudanar da hidindimuna na siyasa cikin ka’idojin bin doka da oda duk da irin tunzurani da suke yi.” Inji Sanata Kabiru Marafa.

Marafa ya cigaba da cewa duk da irin gadar zaren da gwamnatin jahar Zamfara ke yi masa, ya samu nasarar jagorantar gangamin siyasa mafi karfi kuma cikin zaman lafiya a jahar Zamfara, don haka suke bakin cikin goyon bayan da yake da shi a tsakanin al’ummar jahar.

Daga karshe Marafa yace ba zai taba baiwa jama’ansa kunya ba, kuma yana godiya ga irin gudunmuwar da suke bashi, don haka idan har suka zabe shi, ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen ganin ya gyara duk matsalolin da suke fuskanta a jahar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa za ta koma LEGIT.ng Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel