2019: Jerin wasu jiga-jigan 'yan siyasa 10 da ba za su koma majalisa ba

2019: Jerin wasu jiga-jigan 'yan siyasa 10 da ba za su koma majalisa ba

Al'addar gwamnoni da yawa ne a Najeriya su tafi majalisar dattawa a matsayin Sanatoci da zarar sun kammala mulkinsu sau biyu a jihohinsu, duk da yake cewar majalisa ba ta kayyade adadin shekarun da mutum zai iya cigaba da zama ba, akwai alamun wasu tsaffin gwamoni ba za su koma majalisar ba.

Wasu daga cikin gwamnonin da ba za su koma majalisar ba sun hada tsaffin gwamonin Zamfara da Yobe, Ahmed Sani Yarima da Bukar Abba Ibrahim saboda gwamnonin jihohinsu sun yunkuro domin karbe kujerun.

Bayan su akwai wasu Santocin da zai yi wuya su koma majalisar saboda sun rasa tikitin takarar yayin gudanar da zaben fidda gwani na jam'iyoyinsu.

Ga jerin sunayen Sanatocin da kuma dalilin da yasa ba za su koma majalisa ba:

1. Ahmed Sani Yarima

Majiyar Legit.ng ta gano cewar akwai wata yarjejeniya da aka kula tsakanin Yarima da Yari na cewar Yarima zai zabi gwamna da zai gaji Yari yayinda shi kuma ya bawa Yari damar maye gurbinsa a majalisar.

Sai dai a halin yanzu Yari a zabi kwamishinansa, Mukhtar Shehu Idris domin maye gurbinsa kuma ya sayi tikitin takarar kujerar Sanata na yankin Zamfara ta Yamma.

2. Bukar Abba Ibrahim

Duk da cewa a baya Bukar Abba Ibrahim ya yi barazanar cewar zai cigaba da kasancewa a majalisar idan yana so, 'ya'yan jam'iyyar a jihar sun karkata ga gwamna Geidam, hakan yasa Ibrahim ya bayyana cewar ya janye wa Geidam takarar.

3. Ben Murray Bruce

Ben Bruce yana da ya daga cikin Sanatocin da suka shahara a majalisar saboda yakan tofa albarkacin bakinsa a kan abubuwan da ke gudana a kasar.

Duk da cewa ya sayi fom din sake takara, ya janye takararsa bayan mutanen yankinsa sun bayyana cewar tsarin karba-karba suke amfani da ita koma yanzu lokacin wani yanki ne ba na su ba.

DUBA WANNAN: Idan da ni barawo ne da tuni Buhari ya garkame ni a kurkuku - Atiku

4. Abu Ibrahim

Sanata Abu Ibrahim mai wakiltan Katsina ta Kudu na cikin tsaffin Sanatoci da suke dade a majlisa, a baya dan majlisar ya ce zai hakura da takarar amma mutanensa suka tilas masa sai dai yanzu ya cimma matsayar ficewa daga takarar.

5. Aliyu Sabi Abdullahi

Sabi Aliyu yana daya daga cikin na hannun daman Saraki dai rahottani sun nuna cewar mutanen mazabar shi ba su goyon bayansa domin an taba cewa har jifansa da duwatsu aka yi.

Ya sayi fom din sake takara amma ya fadi a zaben fidda gwani a mazabarsa na yankin Niger ta Arewa.

6. Rafiu Ibrahim

Sanata Rafiu Ibrahim mai wakiltan Kwara ta Kudu ya kwashe watanni yana kamfe amma daga bisani aka umurci sa ya janye domin gwamnan jihar Kwara mai barin gado, Abdulfatai Ahmed shima zaiyi takarar Sanata na wannan mazabar.

7. David Umaru

Sanata David Umaru mai wakiltan Niger ta Kudu ya rasa tikitin sake takara bayan ya sha kaye a zaben fidda gwani na jam'iyyarsa.

8. Joshua Lidani

Tsohon mataimakin gwamna kuma Sanata mai wakiltan Gombe ta Kudi ba zai koma majalisa ba saboda ya sha kaye a zaben fidda gwani na jam'iyyar PDP a mazabarsa.

9. Umaru Kurfi

Kamar wasu a cikin jerin Sanatocin da muka ambato, Umaru Kurfi daga jihar Katsina ya sha kaye a zaben fidda gwani na jam'iyyarsa ta APC.

10. Baba Kaka Garbai

Garbai ya tafi majalisa ne bayan rasuwar Sanata Zannah Bukar, sai dai shima ya yi rashin sa'a domin ya fito daga mazaba daya da Gwamnan Borno mai barin gado, Kashim Shettima.

Jam'iyyar ta bukaci Garbai ya janye domin Shettima ya maye gurbinsa a majalisar na tarayya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel