Bayan kusan wata 3: Majalisa za ta dawo daga hutu gobe, za ta kara tafiya wani hutun

Bayan kusan wata 3: Majalisa za ta dawo daga hutu gobe, za ta kara tafiya wani hutun

Majalisar tarayya; majalisar wakilai da ta dattijai, za ta dawo daga hutun ta na shekara da ta tafi a gobe, Talata. Sai dai zata daga zamanta na gobe zuwa jibi, Laraba, saboda mutuwar mamba a majalisar wakilai, Honarabul Funke Adedoyin.

Majalisar zata dawo ne cikin rigingimun yunkurin canja shugabancin majalisun tarayya da mambobin jam’iyyar APC ke shirin yi.

Tun a ranar 24 ga watan Yuli ne majalisar ta tafi hutun da ta ke saka ran zai kare a cikin watan Satumba. Sai dai majalisar ta kara wa’adin hutun da makonni biyu domin bawa mambobinta dammar fafatawa a zabukan fitar da ‘yan takara da aka yi a jam’iyyu daban-daban.

Bayan kusan wata 3: Majalisa za ta dawo daga hutu gobe, za ta kara tafiya wani hutun
Majalisar Najeriya
Asali: Twitter

Ko a wurin taron gangami na jam’iyyar APC na ranar Asabar domin tabbatar da shugaba Buhari a matsayin dan takarar shugaban kasa, said a shugaban masu rinjaye a majalisar dattijai, Ahmed Lawan, da mataimakin shugaban majalisar wakilai, Yusuf Lasun, su ka bayyana cewar APC ce ke da rinjaye a majalisun kasar nan, a saboda haka zasu tabbatar cewar jam’iyyar c eke shugabanci a zauren majalisun kasar nan.

DUBA WANNAN: 2019: Duba sabbin zafafan hotunan shugaba Buhari na yakin neman zabe

Kazalika ‘yan majalisar biyu sun bayar da tabbacin cewar majalisar zata tursasa shugabanninsu domin zartar da kasafin kudin hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) da kuma na hukumomin tsaro.

Sai dai wata kungiya ta mambobin majalisar wakilai dake goyon bayan shugaban majalisar, Yakubu Dogara, ta gargadi mambobin jam’iyyar APC da su jingine batun tsige shi domin ba zasu yi nasara ba .

Kungiyar, ta bakin Honarabul Timothy Golu, ta bayyana cewar mambobin APC da dama zasu fita daga jam’iyyar bayan dawowar majalisar daga hutu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel