Abun kunya: ‘Yan takarar APC sin bawa hammata iska a Zamfara, hoto

Abun kunya: ‘Yan takarar APC sin bawa hammata iska a Zamfara, hoto

Sabani kan hanyar da za ai amfani da ita wajen fitar da ‘yan takara a jam’iyyar APC a jihar Zamfara ya kai ga bawa hammata iska tsakanin ‘yan takara.

Rikicin ya afku ne bayan an gaza cimma daidaito a kan tsarin da a ai amfani das hi wajen fitar da ‘yan takarar a jam’iyyar APC.

Tun da fari sai da kwamitin tsara zaben da uwar jam’iyyar APC ta turo ya fitar da tsarin da za a yi amfani da shi don gudanar da zaben, amma sai bangare na ‘yan takarar suka nuna rashin gamsuwa da tsarin, lamarin ya jawo barkewar cece-kuce da musayar yawu da ta kai ga har an bawa hammata iska.

Kwamitin zaben ya amince da gudanar da zaben ne ta hanyar kai tsaye, da ake kira kato bayan kato, amma sai bangaren masu adawa da dan takarar da gwamna Yari ya tsayar suka bayyana shakku a kan sharudan da kwamitin ya zayyana za ai amfani da su kafin gudanar da zaben.

Abun kunya: ‘Yan takarar APC sin bawa hammata iska a Zamfara, hoto
‘Yan takarar APC sin bawa hammata iska a Zamfara
Asali: Twitter

Shi dai kwamitin ya gindaya sharadin cewar sai an tabbatar da sunan mutum a rajistar jam’iyya kafin a amince ya bi layi domin kidaya shi sannan sun nemi a kawo masu wasu ma’aikata daban da zasu gudanar da aikin zaben.

DUBA WANNAN: An kara kashe wani sojan Najeriya a jihar Filato

Wadannan sharuda ne bangaren masu adawa dad an takarar gwamna suka ce sam basu amince da su ba, su na masu nuna shakku a kan gaskiyar rajistar ‘yan jam’iyya da kwamitin ke shirin amfani da ita.

Tuni dai wasu masu nazarin siyasa ke jin tsoron cewar APC zata iya rasa dan takarar gwamna a jihar Zamfara, musamman ganin cewar yau ne hukumar zabe ta tsayar a matsayin rana ta karshe da zata karbi sunayen ‘yan takara daga jam’iyyu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel