Zaben Fidda Gwani: 'Dan Majalisar Wakilai ya lallasa 'Dan uwansa wajen lashe tikitin takara na jam'iyyar PDP a jihar Kano

Zaben Fidda Gwani: 'Dan Majalisar Wakilai ya lallasa 'Dan uwansa wajen lashe tikitin takara na jam'iyyar PDP a jihar Kano

Mun samu rahoton cewa, Alhaji Nasiru Sule Garo, dan majalisa mai wakilcin mazabar kananan hukumomin Kabo da Gwarzo a majalisar wakilai, ya lallasa kanin sa wajen lashe tikitin takarar kujerar na jam'iyyar adawa ta PDP.

Zaben Fidda Gwani: 'Dan Majalisar Wakilai ya lallasa 'Dan uwansa wajen lashe tikitin takara na jam'iyyar PDP a jihar Kano
Zaben Fidda Gwani: 'Dan Majalisar Wakilai ya lallasa 'Dan uwansa wajen lashe tikitin takara na jam'iyyar PDP a jihar Kano
Asali: Depositphotos

Alhaji Nasiru wanda babban yaya ne ga uwargidan sanatan Kano ta Tsakiya, Rabi'u Kwankwaso, ya yi nasara kan karamin kanin sa, Faruk Sule-Garo yayin zaben fidda gwani na jam'iyyar da aka gudanar cikin Kanon Dabo.

Baturen zaben Dakta Salisu Muhammad Tudunkaya, shine ya bayyana hakan yayin ganawarsa da manema labarai da cewa, Nasiru ya lashe zaben da kuri'u 173 inda dan uwansa ya tashi da kuri'u 12 kacal.

KARANTA KUMA: Tsaro ya yi tsanani yayin zaben fidda gwanin takarar Kujerar gwamna a jihar Imo

Ya ci gaba da cewa, wakilan jam'iyyar 198 da aka tantance sun kada kuri'u yayin zaben inda aka kuma kayyade kuri'u 13 a matsayin wadanda suka gurbata yayin gudanar da zaben.

Kazalika jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya janye takararsa ta sake neman kujerar sa karo na biyu a yayin babban zabe na 2019.

Na nan tafe, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika muna mika godiyar mu ta musamman a gare ku yayin da kuke ci gaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel