Jam'iyyar PDP: Dankwambo ya lalasa Kwankwaso, Atiku da Saraki a zaben gwaji

Jam'iyyar PDP: Dankwambo ya lalasa Kwankwaso, Atiku da Saraki a zaben gwaji

- An gudanar da zaben na a dandalin sada zumunta na Facebook a shafin Legit.ng Hausa

- Dubban jama'a masu bibiyar shafin ne suka kada kuri'unsu inda Dankwambo ya doke sauran 'yan takarar

A wani zaben gwaji da aka gudanar a dandalin sada zumunta na Facebook da Legit.ng Hausa ta shirya, Gwamnan jihar Gombe mai ci, Ibrahim Hassan Dankwambo ya lashe wani kwarya-kwaryan zaben fidda gwani na gwaji da aka gudanar.

Sakamakon zaben ya nuna cewa cikin kuri'u 6,239 da aka kada, Dankwambo ya samu kuri'u 96%, sai mai biye masa Rabiu Musa Kwankwaso ya samu 3%, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya samu 1% yayin da shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki bai samu ko kuri'a daya ba.

DUBA WANNAN: An hana ni takara a PDP don na ki amince ayi lalata da ni - Fati Gombe

Zaben gwaji: Dankwambo kayar da Kwankwaso, Atiku da Saraki
Zaben gwaji: Dankwambo kayar da Kwankwaso, Atiku da Saraki
Asali: Twitter

Duk da cewa wannan ba shine zaben fidda gwani na anihi ba, masu hasashen siyasa na amfani dashi wajen iya gano yadda anihin zaben ka iya kasancewa.

A wani labarin, Legit.ng ta kawo muku cewa jam'iyyar APC ta dage lokacin fara babban taron gangaminta da za'ayi a Abuja daga 12 na rana inda ya mayar da shi 6 na yamma.

Jam'iyyar ta ce an dage lokacin ne saboda a bawa deleget din jihohi damar zuwa babban birnin tarayya Abuja domin a fara taron da su.

Akwai wasu jihohin da basu fara zaben fidda gwaninsu kan lokaci ba hakan yasa suka samu jinkiri wajen tattara sakamakon zabukkan.

Sanarwan dage lokacin taron ya fito ne daga bakin ciyaman din kwamitin shirye-shirye na babban taron, Gwamna Abiola Ajimobi na jihar Oyo.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel