'Yan sanda sun damke 'yan bangar siyasa da suka addabi mutane a Kano (Hotuna)
- Yan sanda sun kama wasu 'yan bangan siyasa da suke nemi tayar da tsaye yayin zabukkan fidda gwani a jihar Kano
- An same 'yan bangar da makamai kamar adda, sanduna, wukake, barandami da sauransu
- Hukumar 'yan sanda ta ce za'a mika su zuwa kotu da zarar an kammala bincike domin su fuskanci shari'a
A yau Juma’a ne rundunar ta 'yan sanda reshen jihar Kano ta yi gabatarwa manema labarai wasu 'yan bangar siyasa wadanda aka kama a yayin zabubbukan fidda gwani na jam’iyyu daga Talata 2 zuwa Juma’a 5 ga watan Oktoban 2018.

Asali: Facebook
DUBA WANNAN: 'Yan takarar shugabancin kasa na PDP 5 ne kawai suka hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya
Cikin wadanda aka kama har da wani dan fashi da makami wanda an dade ana nemansa wato Bashir Musa da aka fi sani da Gachi wanda ke addabar Unguwannin Hotoro, Na'ibawa, Mariri da sauransu a birnin Kano.

Asali: Facebook

Asali: Facebook
Kakakin rundunar yansandan jihar Kano, SP Magaji Musa Majia ya ce sun kama 'yan bangar siyasar da mugayen makamai masu yawa da suka hada da adda, barandami, sanduna da wukake. Yace dukkanin yandaban da ke hannun su zasu mika su zuwa kotu domin ayi musu hukunci dai dai da abinda suka aikata.

Asali: Facebook
Daga karshe SP Majia, ya tabbatar da cewa rundunarsu za ta cigaba da aiki ba dare ba rana wajen kame duk wasu 'yan bangar siyasa a Jihar Kano don ganin anyi zaben shekara ta 2019 cikin lafiya da kwanciyar hankali.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng