Jami'ar Dakarun Soji ta yiwa Muhammad Indimi babban Karamci

Jami'ar Dakarun Soji ta yiwa Muhammad Indimi babban Karamci

Za ku ji cewa babbar jami'ar nan mai horas da dakarun soji ta Najeriya watau NDA, Nigeria Defence Academy, ta yiwa Muhammad Indimi babban karamci na Digirin Digirgir watau Digiri na uku yayin bikin yaye dalibanta a jihar Kaduna.

Dakta Indimi wanda shine mai mallaki kuma shugaban katafaren kamfanin nan na Oriental Energy Resources Limited, ya samu wannan karamci yayin bikin yaye sabbin dakarun soji karo na 26 da suka kammala daukan horo da karatu a fannikan nazarin ilimi daban-daban.

Indimi wanda ya kuma kasance Suruki ga shugaban kasa Muhammadu Buhari sakamakon dan sa a yake auren diyar Buhari, Zahra, ya samu wannan karamci ne tare da shugaba bankin African Development Bank, Akinwunmi Adesina.

Kamar yadda shafin jaridar Vanguard ya ruwaito, babban kamfanin na Oriental Energy, shine ya bayar da tabbacin hakan cikin wata sanarwa da bayyana yau Juma'a a babban birnin kasar nan na tarayya.

Jami'ar Dakarun Soji ta yiwa Muhammad Indimi babban Karamci
Jami'ar Dakarun Soji ta yiwa Muhammad Indimi babban Karamci
Asali: UGC

Sanarwar katafaren kamfanin ta bayyana cewa, Jami'ar ta karrama wannan manyan Mutane biyu sakamakon kasancewar zakarun gwajin dafi da kuma fice da suka yi wajen bautawa kasar nan ta Najeriya ta fuskar bayar da muhimmiyar gudunmuwa da taka rawar gani wajen inganta zamantakewa da kuma habaka tattalin arziki.

Cikin wata hikayar zance da Kwamandan jami'ar Sojin ya zayyana, Manjo Janar Adeniye Oyebade ya bayyana cewa Indimi ya samu wannan babban karamci ne a sakamakon kasancewar wani Madubi ga harkokin kasuwanci a nahiyyar Afirka.

KARANTA KUMA: Hukumar INEC ta rarrashi fusatattun shugabanni na jam'iyyar PDP yayin zanga-zangar su

A yayin bayyana farin cikin sa gami da godiya, Dakta Indimi ya kwarara yabo dangane da wannan karamci da cewar ya cimma buri da muradin zuciyar sa na taka rawar gani wajen inganta zamantakewar al'umma tare da bayar da gudunmuwa wajen habaka tattalin arzikin kasar nan.

Legit.ng da sanadin kamfanin dillancin labarai na Najeriya ta fahimci cewa, Dakra Indimi ya yi bajinta bila adadin a fadin kasar kama daga sadaukar da kai da taimako na bayar da masauki ga 'yan gudun hijira na Bama a jihar Borno zuwa ga bayar da tallafi na ilimi, lafiya gami da sana'a da a halin yanzu dubunnan Mutane ke amfana.

Nan ba da jimawa ba, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika muna mika godiyar mu ta musamman a gare ku yayin da kuke ci gaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel