Gwamnatin tarayya za ta jinginar da manyan tashohin sauka da tashin jiragen Najeriya

Gwamnatin tarayya za ta jinginar da manyan tashohin sauka da tashin jiragen Najeriya

Gwamnatin tarayya ta fara shirin jinginar da manyan filayen sauka da tashin jiragen sama na Najeriya ga yan kasuwa da zasu tafiyar da shi ta hanyar daya kamata na tsawon shekaru talatin masu zuwa, inji rahoton jaridar Daily Trust.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito ministan sufurin jiragen sama, Hadi Suruka ne ya bayyana haka a ranar Juma;a 5 ga watan Oktoba a yayin bikin bude katafern otal na Legend Hotel Lagos Curio Collectn na kamfanin Hilton.

KU KARANTA: Siyasa mugun wasa: Murnar Sanata Shehu Sani ta koma ciki game da zaben fidda gwani

Gwamnatin tarayya za ta jinginar da manyan tashohin flayen sauka da tashin jiragen Najeriya
Tashar
Asali: Depositphotos

A jawabinsa, Sirika ya bayyana cewa nan da karshen watan Oktoba ne za’a kaddamar da fara aikin sabbin hanyoyin jiragen saman da Najeriya ta gina a filayen sauka da tashin jirage na Muratala Muhammed dake Legas, sai kuma na Fatakal da na Abuja wanda bankin China ta dauki nauyin aikinsu, tashar jirgin sama na Kano ma za’a gyarata.

“Wannan Otal din ya kasance kayatacce ba don komai ba sai don kasancewarsa tazarar taku goma zuwa shiga jirgi, wanda hakan yasa ya zamto daya tamkar da dubu a nahiyar Afirka gaba daya, ina tabbatar muku mun fara kenan har sai mun inganta filayen jiragen saman Najeriya da makamantansa.

“Amma fa ku sani burin gwamnatinnan shine ta jinginar da filayen sauka da tashin jiragennan, muna ganin gwamnati ba za ta iya tafiyar da filayennan yadda ya kamata ba don haka zamu mikasu ga yan kasuwa, zamu jinginar dasu na tsawon shekaru 25-30.” Inji Hadi.

Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai shugaban kamfanin Hilton na duniya gaba daya, Christopher Nasette, shugaban kamfanin Dangote, Aliko Dangote, shugaban bankin Access, Herbert Wigwe da shugaban Oando, Wale Tinubu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa za ta koma LEGIT.ng Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel