Rikicin Jos: Gwamnati jahar Taraba ta kwashe daliban jahar 383 dake karatu a Jami’ar Jos

Rikicin Jos: Gwamnati jahar Taraba ta kwashe daliban jahar 383 dake karatu a Jami’ar Jos

Gwamnatin jahar Taraba ta kwashe dalibai yan asalin jahar dake karatu a jami’ar gwamnatin tarayya dake garin Jos na jahar Filato don gudun kada rikicin kabilanci da na addinin da ake samu a garin ya shafesu kamar yadda kamfanin dillancin labaru, NAN, ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito mashawarcin gwamnan jahar Taraba Darius Ishaku akan harkokin dalibai, Samson Tor-Musa ne ya sanar da haka ga manema labaru a garin Jalingo a ranar Juma’a 5 ga watan Satumba, inda yace gwamnatin ta dauki matakin ne biyo bayan samun labarin kashe wani dalibin jami’ar guda daya.

KU KARANTA: Hukumar EFCC ta tasa keyar Sanata gaban kotu kan zargin wawure naira miliyan 322

Rikicin Jos: Gwamnati jahar Taraba ta kwashe daliban jahar 383 dake karatu a Jam’ar Jos
Jami’ar Jos
Asali: UGC

Musa ya bayyana ma yan jaridu cewa wannan matakin ya zama wajibi musamman duba da yadda daliban jami’ar yan asalin jahar Taraba suka yi kira ga gwamnatin jahar da ta kawo musu dauki, hakan ta sanya gwamnatin amsa kirarsu, inda ta kwashe dalibai dari uku da tamanin da uku.

Mista Musa ya cigaba da bayyana cewa sakamakon gano motar wani babban sojan Najeriya a cikin wani rafi ne ya kara rura rikicin da ake samu a cikin jami’ar, wanda ya sabbaba mutuwar dalibi daya a makarantar.

“Rafin aka gano motar Sojan na kusa da wani rukucin dakunan daliban jami’ar ne, don haka sai hankula suka tashi, kuma zuwa yanzu jami’ar ta tabbatar da mutuwar dalibi daya, amma a lokacin da muka isa makarantar, sai muka tarar akwai wani dalibin jami’ar dan asalin garin Takum da shima an kashe shi sakamakon hatsaniyar.

“Don haka muka kwashe dalibai 383 daga cikin 423 dake karatu a makarantar, yayin da sauran cikon dalibai 40 suka wuce gidajensu dake jahar Taraba tun ma kafin mu isa makarantar.” Inji shi.

Daga karshe Musa yace ganin halin da suka tsinci daliban jahar sun tausaya musu matuka, kuma tuni sun mika hannun iyayensu, da wannan ne guda daga cikin iyayen daliban, Andetarang Irammae ya jinjina ma matakin da gwamnatin jahar ta dauka

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa za ta koma LEGIT.ng Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel