An yankewa wani Matashi hukuncin dauri na shekaru 10 bisa laifin Kashe 'Dan Uwansa a garin Legas

An yankewa wani Matashi hukuncin dauri na shekaru 10 bisa laifin Kashe 'Dan Uwansa a garin Legas

A jiya Laraba da Hausawa kan ce Tabawa ranar samu wata babbar kotu dake garin Ikeja na jihar Legas, ta samu nasarar yankewa wani matashi dan shekara 28 hukuncin dauri na zama a gidan sarka har na tsawo shekaru 10 bisa aikata laifi na kisan kai.

Kotun ta yankewa Misa Collins Abakwe hukuncin cin sarka na tsawon shekaru goma bisa laifin batar da dan uwan sa daga doron kasa a sanadiyar sa'insa kan wata Mace bakuwa da suka yi, inda suka yi cacar baki kan wanda zai rage dare da ita.

Alkaliyar Kotun, Raliat Adebiyi, ita ta zartar da wannan hukuncin kan Mista Collinsa a bisa laifin kisan gillar da ya aikata tun a shekarar 2013 da ta gabata kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito.

An yankewa wani Matashi hukuncin dauri na shekaru 10 bisa laifin Kashe 'Dan Uwansa a garin Abuja
An yankewa wani Matashi hukuncin dauri na shekaru 10 bisa laifin Kashe 'Dan Uwansa a garin Abuja
Asali: Facebook

A yayin zayyana shaidarta a gaban kotun, ma'aikaciyar ta hukumar 'yan sanda Misis O. A Olugasa ta bayyana cewa, Mista Collins ya aikata wannan babban laifi a ranar Masoya da ta yi daidai da 14 ga watan Fabrairu na shekarar 2013, inda ya bude Tumbin dan uwansa da wata fasasshiyar kwalba.

KARANTA KUMA: Akwai yiwuwar Najeriya za ta fuskanci karancin Shinkafa a 2019 - Audu Ogbeh

Bincike ya tabbatar da cewa wannan laifi na amfani da makami wajen aikata ta'addanci ya sabawa sassa na 221 da kuma 227 cikin dokokin jihar Legas.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito, jami'an 'yan sanda sun tirnike shugabannin jam'iyyar PDP da Barkonon Tsohuwa a yayin da suke gudanar da zanga-zanga zuwa shelkwatar hukumar zaben ta kasa watau INEC dake babba birnin kasar nan na Abuja.

Na nan tafe: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mu na ci gaba da godiya a yayin kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel