Yara 13.2m ne basu zuwa makaranta a kasar nan, inji UBEC

Yara 13.2m ne basu zuwa makaranta a kasar nan, inji UBEC

- Almajirici dai ya zama al'adar 'yan Najeriya

- Babar Shekau ma tace daga boko aka cire shi aka maida shi almajiri

- Yaran kanyi gararamba a tituna don neman abinci

Yara 13.2m ne basu zuwa makaranta a kasar nan, inji UBEC
Yara 13.2m ne basu zuwa makaranta a kasar nan, inji UBEC
Asali: Depositphotos

Binciken da kungiyar Demographic Health Survey(DHS) ta yi a 2015, ya nuna yara 13,200,000 nebasu zuwa makaranta, wanda ya tashi daga 10,500,000 a tsohon bincike da aka yi a 2010. Sai a yanzu a 2018 aka iya sakin rahoton, bayan da UNICEF da UBEC suka amince da shi.

Boko Haram dai ta lalata dubban makarantu, kusan a duk jihohin da abin ya shafa a arewa maso gabas.

Amma ko ba don boko haram ba, arewacin Najeriya bai damu da ilimin yara ba, musamman na mata, inda ake ganin ai su kawai aure ya kamata ayi musu basu bukatar tsaya wa da kafarsu.

DUBA WANNAN: EFCC ta kwato 1.5 daga Neja Delta

A taron da za'ayi a tsakiyar watan nan, tsakanin UBEC, hukuma mai kula da karatun yara, da UNICE, mai kula da harkokin yara a duniya, za'a zauna da sarakunan gargajiya a KAduna, inda za'a yi kokarin wayar musu da kai domin su wayar wa da jama'arsu kai kan illar hakan.

A wannan lokaci na siyasa dai, sai dai a raba manyan motoci, a kashe biliyoyin kudi, ayi biki ayi rawa, a zabi na zaba, a kayar da na kayarwa, shuwagabanni su shiga manyan motoci, amma su bar yara barkatai a gidajen mai da tituna suna neman na abinci.

Kaico!

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mungode da kasancewanku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel