Buhari ya gwale Oshiomhole: Babu wanda zamu ba tikiti ba tare da zaben cikin gida ba

Buhari ya gwale Oshiomhole: Babu wanda zamu ba tikiti ba tare da zaben cikin gida ba

- Ana shirye-shiryen gudanar da zaben fidda gwani na masu neman takarar sanata da majalisan wakilan tarayya a jihar Kaduna

- Wannan na zuwa ne bayan shugaba Muhammadu Buhari ya soke tikitin takara kai tsaye da Adams Oshiomhole ya bawa wasu 'yan takara a jam'iyyar

- A halin yanzu dai 'yan takara suna shirye-shiryen gudanar da zaben fidda gwanin gabanin babban taron APC da za ayi ranar 6 ga watan Oktoba

'Yan siyasa a jihar Kaduna suna ta gudanar da taruruka da wakilan jam'iyyar APC da sauran masu ruwa da tsaki domin shirin gudanar da zaben fidda gwani na masu neman takarar kujerar majalisar wakilai na tarayya da sanata kamar yadda Politics Today ta ruwaito.

Wata kwakwarar majiya daga jam'iyyar ta APC ta ce tuni an gama shirye-shirye kuma masu neman takarar suna ta ganawa da magoya bayansu tun a daren jiya Alhamis domin tabbatar da cewar sunyi nasara.

Zaben cikin gida: Buhari ya taka wa Oshiomhole birki, ya ce babu wanda za'a bawa tikitin takara kai tsaye
Zaben cikin gida: Buhari ya taka wa Oshiomhole birki, ya ce babu wanda za'a bawa tikitin takara kai tsaye
Asali: Depositphotos

Wannan na zuwa ne bayan shugaba Muhammadu Buhari ya umurci Ciyaman din jam'iyyar, Adams Oshiomhole da ya janye alkawarin bayar da tikitin takara kai tsaye da ya yiwa wasu masu neman takarar kujerar Sanata jam'iyyar a cewar News Diary.

DUBA WANNAN: Tana kasa tana dabo: Kotu ta takawa APC burki a kan zaben Shehu Sani

Kazalika, gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya yi wata ganawar sirrri da shugaba Muhammadu Buhari a fadar Aso Villa da ke Abuja inda ake kyautata zaton ya yi korafi kan matakin da Oshiomhole ya dauka a baya na bawa wasu tikitin takara kai tsaye.

Har ila yau, wata majiyar ta ce 'yan siyasa da magoya bayansu suna ta kaiwa da komowa da hedkwatan APC da ke Ali Akilu Way domin kammala shirye-shiryen zaben.

Mallam Uba Sani wanda shine dan takarar da ya fi barazana ga kujerar Sanata Shehu Sani wadda ya ke neman zarcewa kan kujerarsa ta wakilcin mazabar Kaduna ta Tsakiya a majalisar dattawa na tarayya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel