An binne yayan jam’iyyar APC 5 da suka mutu a sanadiyyar rikicin jahar Zamfara

An binne yayan jam’iyyar APC 5 da suka mutu a sanadiyyar rikicin jahar Zamfara

Akalla mutane biyar ne suka mutu a sanadiyyar rikicin siyasar APC da ta barke a jahar Zamfara a yayin gudanar da zaben fidda gwani daya gudana a ranar Laraba 3 ga watan Oktoba, kamar yadda jaridar Daily trust ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito a ranar Alhamis 4 ga watan Oktoba ne aka binne gawarwakin jama’an su biyar, wanda ya samu halartan jama’a da dama daga ciki har da mataimakin gwamnan jahar Zamfara kuma daya daga cikin yan takarkarun gwamna, Ibrahim Wakkala.

KU KARANTA: Yan APC a majalisa sun bayyana matakin da zasu dauka akan Dogara da zarar ya bude majalisa

Daga cikin mamatan akwai wani dalibin jami’ar gwamnatin tarayya na Gusau, Samaila Sani Afro, haka zalika akwai jama’a da dama da suka samu munanan rauni a sakamakon harbe harben bindiga, da saran adduna, da a yanzu haka suke samun kulawa a asibitoci.

Sai dai kaakakin rundunar Yansandan jahar ya sanar da kama wasu mutanen da take zargi da aikata wannan mummunan aiki.

A wani labarin kuma, uwar jam’iyyar APC ta kasa ta dage gudanar da zaben fitar da dan takarar gwamnan jahar Zamfara biyo bayan tashin tashinan da aka samu a garuruwan Gusau da Bungudu na a sanadiyyar rashin kawo aikin da za’a gudanar da zaben

Wani ma’abocin kafar sadarwar zamani ra Facebook, Abdulrahman ne ya bayyana wasu hotuna a shafinsa dake nuna fusatattun matasa yayin da suke kona tayoyi akan titi suna furta muggana kalamai ga shuwagabbanni.

Wata majiya ta ruwaito cewa rashin fara gudanar da zaben na APC akan lokaci ne ya fara harzuka matasan, amma a lokacin da jami’an zaben suka hallara garin Bagudu, sai aka lura cewa takardun kuri’un da suka zo da shi bai adadin jama’an da suka fito ba, hakan ya kara harzuka matasa inda suke ganin an shirya cutansu ne.

Da kyar da sudin goshi aka samu jami’an rundunar Yansanda suka kwantar da tarzomar, ta hanyar harba harsashi a sama da kuma harba barkonon tsohuwa, da haka ne matasan suka tarwatse.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa za ta koma LEGIT.ng Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel