Rundunar Sojin Najeriya ta kulla alakar aiki da horo da rundunar Sojin kasar Pakistan

Rundunar Sojin Najeriya ta kulla alakar aiki da horo da rundunar Sojin kasar Pakistan

Rundunar Sojan kasar Najeriya ta nuna sha’awarta ta kulla kyakkyawar alaka tsakaninta da rundunar sojojin kasar Musulunci ta Pakistan ta bangarorin tattara bayanan sirri, samar da horo, sadarwar, taimakon makamai da sauransu.

Legit.ng ta ruwaito shugaban hafsoshin rundunar Sojan kasa ta Najeriya, laftanar janar Tukur Yusuf Buratai ne ya bayyana haka a lokacin da ya karbi bakoncin jakadan kasar Pakistan a Najeriya manjo janar Wagar Ahmed Kingravi mai murabus.

KU KARANTA: Yan APC a majalisa sun bayyana matakin da zasu dauka akan Dogara da zarar ya bude majalisa

Rundunar Sojin Najeriya ta kulla alakar aiki da horo da rundunar Sojin kasar Pakistan
Buratai da Wagar
Asali: Facebook

A jawabinsa, Buratai ya tuna cewa Najeriya da kasar Pakistan na da kyakkyawar alaka da fahimtar juna ta bangaren abinda ya shafi harkar Soji, musamman ta horas da manya da kananan Sojojin Pakistan a Najeriya.

Da wannan ne Buratai ya yi kira ga kasashen biyu da su cigaba da wannan alakar, inda yace Najeriya a shirye take ta cigaba da mutunta wannan kyakkawar alakar domin ta amfana daga kwarewar rundunar sojan Pakistan wajen yaki da ta’addanci.

Haka zalika Buratai ya yaba ma Pakistan da taimakon da ta baiwa Najeriya wajen samar da na’urorin sadarwa na rediyo, wanda yace sun taimaka ma Sojojin Najeriya matuka a nasarorin da suka samu a yaki da Boko Haram.

Rundunar Sojin Najeriya ta kulla alakar aiki da horo da rundunar Sojin kasar Pakistan
Zaiyarar
Asali: Facebook

Shima a nasa jawabin, Manjo janar Wagar ya jinjina ma Buratai game da yadda ya bashi kyakkyawar tarba, inda ya kara da cewa yana alfahari da kyakkyawar alakar dake tsakanin kasarsa da Najeriya musamman ta bangare Soji.

Bugu da kari Wagar ya yaba da kokarin da Sojojin Najeriya suke yi a karkashin jagorancin Buratai a yaki da kungiyar ta’addanci ta Boko Haram, sa’annan ya yi kira ga Najeriya da ta nemi agajin Pakistan domin horas da Sojojinta sakamakon kasar na da kwarewa a yaki da ta’addanci.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa za ta koma LEGIT.ng Hausa

Asali: Legit.ng

Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel