Assha: Wani asararen mahaifi ya dirka wa diyarsa mai shekaru 13 ciki

Assha: Wani asararen mahaifi ya dirka wa diyarsa mai shekaru 13 ciki

Hukumar 'yan sanda reshen jihar Edo ta kama wani magidanci, Friday Moses da ake zargin yana saduwa da karamar diyarsa mai shekaru 13 har ta kai ga yarinyar da sami juna biyu.

Moses yana daya daga cikin wasu da ake zargi da aikata laifuka 76 ga Kwamishinan 'yan sandan jihar, Johnson Babatunde Kokumo ya gabatarwa manema labarai a jihar.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito cewa Moses wanda dan asalin jihar Cross Rivers ne amma yana zama a Edo ya fara saduwa da diyarsa ne tun tana da shekaru 7 a duniya.

Assha: Wani asararen mahaifi ya dirka wa diyarsa mai shekaru 13 ciki
Assha: Wani asararen mahaifi ya dirka wa diyarsa mai shekaru 13 ciki
Asali: Twitter

An gano cewa jama'ar garin Ologbo da ke karamar hukumar Okha na jihar Edo sun kore shi daga garin bayan sun gano yana saduwa da diyar cikinsa.

DUBA WANNAN: Kwamishiniya a Gombe ta tika kawunta da kasa a zaben cikin gida na PDP

Haka yasa Moses ya koma unguwar Egba da ke karamar hukumar Ipoha Okha inda ya cigaba da aikata wannan mummunan dabi'a har sai ta diyarsa ta samu juna biyu.

Bayan mutanen unguwa sun gano abinda ke faruwa tsakanin diyar da mahaifinta ne suka garzaya ofishin 'yan sanda suka shigar da kara kana daga baya aka kama shi.

A yayin da ta ke magana da manema labarai, yarinyar ta aka ce tana dauke da cikin watanni biyar ta ce mahaifinta ya fara saduwa da ita tun tana karamar yarinya kuma ya yi barzanar zai kashe ta idan ta fadawa mutane.

Sai dai wanda ake tuhumar ya musanta cewar shine ya yiwa diyarsa ciki inda ya kara da cewa matarsa da rasu shekaru 5 da suka wuce amma daga baya ya sake samun wata budurwa wadda daga baya sun rabu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel