Akwai sa hannun Manyan kasa a rikicin Filato - Inji Janar Buratai
Mun ji cewa Shugaban Hafsun Sojin Najeriya Tukur Buratai ya bayyana cewa shakka babu akwai sa-hannun wasu manya a rikicin da ke aukuwa a Jihar Filato wanda ya ki ci ya kuma ki cinyewa.

Asali: Twitter
Laftana Janar Tukur Buratai ya fito ya nuna cewa manyan Gari sun san abin da ke faruwa a Filato inda ake cigaba rigimar da tayi sanadiyyar rasa rayuka da-dama. Buratai ya bayyana wannan ne lokacin da aka birne wasu Sojojin kasar.
Shugaban Hafsun Sojojin kasan na Najeriya ta bakin Jagoran Rundunar Sojin Operation Safe Haven watau Manjo Janar Augustine Agundu ya fasa kwan abubuwan da ke aukuwa a Filato inda yace wasu manya ke kitsa wannan aiki.
KU KARANTA: An gano motar Janar din sojan da ya bace kwanaki a Jos
Kamar yadda mu ka ji, Janar Agundu yace manyan Jihar ne ke amfani da Matasa wajen tada rikicin da yake sanadiyyar rasa rayukan al’umma. Agundu yace Mala’un Yankin sun san duk abin da ke faruwa kuma akwai hannun sa a lamarin.
Kwanan nan dai rikici ya barke a wani kauye kusa da barkin Ladi inda aka kashe har Jami’an tsaro. Daga cikin Sojojin da aka rasa akwai Effiong Mbuotidem, Isah Ojaghale Kingsley Aloue wanda aka birne su jiya a Makabartar Sojoji a Jos.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.
Mun gode da kasancewar ku tare da mu.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng