Al’ummar garin da aka gano motar Janar Alkali sun fara yin gudun hijira don gudun hukuncin Soja

Al’ummar garin da aka gano motar Janar Alkali sun fara yin gudun hijira don gudun hukuncin Soja

Al’ummar garin dake garin Du dake karamar hukumar Jos ta kudu sun fara tserewa daga garin nasu don tsoron hukuncin da iya hawansu sakamakon gano motar wani babban jami’in Soja da aka yi a cikin wani korama dake garinsu, kuma an nemi sojan an rasa.

Wata ma’abociyar kafar sadarwar zamani, Zara Gift Oyinye ce ta daura hotunan matan garin yayin da suke ficewa daga garinnasu zuwa wasu sassan jahar Filato don tsira daga hukuncin da suke tunanin zai iya hawansu.

KU KARANTA: Rikici ya barke a jahar Zamfara saboda zaben fidda gwanin takarar gwamna

Kimanin sati uku da suka gabata ne aka nemi janar IB Alkali, wanda shine daraktan kudi da mulki na rundunar sojan kasa, amma ba’a same shi ba, sai dai bincike ya nuna inda aka ganshi na karshe shine hanyar Bauchi a garin Jos.

Al’ummar garin da aka gano motar Janar Alkali sun fara yin gudun hijira don gudun hukuncin Soja
Al’ummar garin Du
Asali: UGC

Haka ne yasa Sojoji suka fara gudanar da bincike a yankin, har suka kai ga wata korama dake garin Du wanda suke zargin za’a iya samun gawar Sojan a cikin ta, sai dai jama’an garin, musamman mata sun gudanar da zanga zanga sun nuna rashin amincewa da binciken Sojojin, inda suka ce suna bauta a koramar.

Amma duk da zanga zangar da matan suka yi, sai da Sojoji suka yashe koramar, anan fa suka gano motar babban Sojan tare da wasu yan kayayyakinsa, amma basu samu gawarsa ba, haka zalika Sojojin sun gano wasu motoci guda uku a cikin koramar, ko a ranar Talata sai da Sojoji suka sake gano wata motar Bus a ruwan.

Wadannan abubuwan da Sojoji suka gano yasa jama’a na zargin wannan shine abinda yan ta’adda daga kabilar Berom ke yi, suna kashe mutane sai su jefa motocinsu a cikin wannan ruwa, amma dai Sojoji basu tabbatar da hakan ba.

A wani labarin kuma, rundunar Sojan kasa ta yi kira ga jama’an garin Du dasu cigaba da zamansu a garinsu ba tare da fargaba ba, matukar sun san basu da hannu cikin bacewar wannan babban sojan, “Zamu cigaba da nemansa har sai mun gano shi ko gawarsa.” Inji wani Soja.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa za ta koma LEGIT.ng Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel