Rikici ya barke a jahar Zamfara saboda zaben fidda gwanin takarar gwamna

Rikici ya barke a jahar Zamfara saboda zaben fidda gwanin takarar gwamna

Rahotannin da Legit.ng ta samu sun nuna cewa a rikici ya barke a garin Bungudu na jahar Zamfara a sanadiyyar rashin kawo aikin da za’a gudanar da zaben fitar da dantakarar gwamnan jahar na jam’iyyar APC akan lokaci.

Wani ma’abocin kafar sadarwar zamani ra Facebook, Abdulrahman ne ya bayyana wasu hotuna a shafinsa dake nuna fusatattun matasa yayin da suke kona tayoyi akan titi suna furta muggana kalamai ga shuwagabbanni.

KU KARANTA: Yadda wani rakumi ya halaka yaro dan shekara 18 a Kebbi a hadarin ‘Taho mu gama

Rikici ya barke a jahar Zamfara saboda zaben fidda gwanin takarar gwamna
Rikici
Asali: UGC

Wata majiya ta ruwaito cewa rashin fara gudanar da zaben na APC akan lokaci ne ya fara harzuka matasan, amma a lokacin da jami’an zaben suka hallara garin Bagudu, sai aka lura cewa takardun kuri’un da suka zo da shi bai adadin jama’an da suka fito ba, hakan ya kara harzuka matasa inda suke ganin an shirya cutansu ne.

Da kyar da sudin goshi aka samu jami’an rundunar Yansanda suka kwantar da tarzomar, ta hanyar harba harsashi a sama da kuma harba barkonon tsohuwa, da haka ne matasan suka tarwatse.

Wannan lamari tare da halin dar dar da ake ciki a jahar Zamfara akan wannan zabe yasa har yanzu ba a ko ina ake gudanar da zaben dan takarar gwamnan na jam’iyyar APC ba, kuma ba komai bane ya rura wannan rikici face dagewa da bangaren gwamnan jahar da na yan adawansa suka yi akan takara.

Rikici ya barke a jahar Zamfara saboda zaben fidda gwanin takarar gwamna
Rikici
Asali: UGC

Shidai gwamnan jahar Abdul Aziz Yari ya rantse sai kwamishinan kudinsa, Alhaji Muktar Idris ya zama gwamnan jahar Zamfara a karkashin inuwar jam’iyyar APC, haka kuma akwai wasu gagga gaggan yan takarar gwamna a jam’iyyar ta APC da suka yi tirjiya ga bukatar gwamanan.

Daga cikin yan takarar gwamnan su takwas dake adawa da Yari akwai Mataimakin gwamna Ibrahim Wakkala, ministan tsaro Mansur Dan Ali, Sanata Kabiru Marafa, tsohon gwamna Mahmud Aliyu Shinkafi, dan majalisa Aminu Sani Jaji, Engineer Abu Magaji, Dauda Lawal da Mohammed Sagir Hamid.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa za ta koma LEGIT.ng Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel