Amsar da Buhari ya bawa wata kasa da ta nemi taimakon Najeriya wajen warware matsalolin ta

Amsar da Buhari ya bawa wata kasa da ta nemi taimakon Najeriya wajen warware matsalolin ta

- Shugaba Buhari ya fadawa Sudan ta Kudu cewar Najeriya tana da matsalolin da ke adabar ta

- Sai dai matsalolin ba za su hana Najeriya taimakawa kasashen da ke bukatar taimakon Najeriya ba

- Buhari ya yi wannan jawabin ne yayin da ya ke tarabar tawagar shugaban kasar Sudan ta Kudu ta suka ziyarce shi a Abuja

A yau, Talata ne shugaba Muhammadu Buhari ya ayyana cewar Najeriya itama tana da wasu matsalolin da ke ci mata tuwo a kwarya amma hakan ba zai hana kasar ta taimakawa Sudun ta Kudu wajen farfado ta tattalin arzikinsu da samar da zaman lafiya mai dorewa.

A cewar wata sanarwa da ta fito daga mai taimakawa shugaban kasa na musamman kan kafafen yada labarai, Femi Adesina, shugaban kasar ya furta wannan magana ne yayin da ya karbi tawagar shugaban kasar Sudan ta Kudu, Mr Ezekiel Gatkuoth a fadar Aso Villa da ke Abuja.

Amsar da Buhari ya bawa wata kasa da ta nemi taimakon Najeriya wajen warware matsalolin ta
Amsar da Buhari ya bawa wata kasa da ta nemi taimakon Najeriya wajen warware matsalolin ta
Asali: Facebook

Shugaba Buhari ya ce kasashen biyu suna fuskantar mastaloli masu kamanceceniya a fannin samar ayyukan cigaba.

DUBA WANNAN: PDP ta bani cin hancin makudan miliyoyi don na bar APC - Sanatar Arewa

"Najeriya tana da matsalolin da ke adabar ta.

"Amma tunda Sudan ta Kudu tana son taimakon Najeriya, za mu cigaba da taimakawa a fanonin da zamu iya kuma muna addu'a samun zaman lafiya a kasar ku," inji Buhari.

Shugaba Muhammadu Buhari ya shawarci shugabanin Sudan ta Kudu su cigaba da sadaukar ka kawunansu har sai lokacin da abubuwa suka daidaita a kasar.

Ya kuma basu shawarar mayar da hankali wajen samar da zaman lafiya da ayyukan yi musamman ga matasa, yaki da rashawa da kuma kokarin habbaka tattalin arzikin kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Online view pixel