Gwamna Abubakar ya lashe zaben fidda gwani na jam'iyyar APC a jihar Bauchi

Gwamna Abubakar ya lashe zaben fidda gwani na jam'iyyar APC a jihar Bauchi

Mun samu rahoton cewa gwamnan jihar Bauchi, Muhammad Abdullahi Abubakar, ya zamto zakaran da ya cafke tikitin takara a zaben fidda gwanin takarar kujerar gwamnan jihar Bauchi na karkashin jam'iyyar APC.

Ko shakka ba bu gwamnan shi ya zamto zakaran gwajin dafi yayin zaben fidda gwani da aka gudanar cikin jihar a ranar Litinin din da ta gabata, inda zai fito kwansa da kwarkwata a babban zabe na 2019.

Kamar yadda shafin jaridar Daily Trust ya ruwaito, an bayyana sakamakon zaben a Yammacin yau na talata inda gwamna Abubakar ya samu kuri'u 75, 086 yayin da ya lallasa abokin takararsa tsohon ministan 'yan sanda, Dakta Ibrahim Lame, wanda ya samu kuri'u 3,988 kacal.

Gwamna Abubakar ya lashe zaben fidda gwani na jam'iyyar APC a jihar Bauchi
Gwamna Abubakar ya lashe zaben fidda gwani na jam'iyyar APC a jihar Bauchi
Asali: Depositphotos

Sai dai tun a daren jiya wasu 'yan takara uku suka fidda da rai da kuma rashin kyautata zato a yayin da zaben ke ci gaba da gudana.

KARANTA KUMA: Atiku ya bayyana dalilin da ya sanya masu madafan iko ke masa adawa

A yayin bayyana sakamakon zaben a babban ofishin jam'iyyar dake jihar Bauchi, Babban Baturen Zaben, Farfesa Ahmed Bakari, ya bayyana cewa gwamna Abubakar ya yi zarra ga sauran manema tikitin takarar kujerar gwamna na jam'iyyar.

Kazalika jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, shugabancin jam'iyyar APC yayi watsi da zaben fidda gwanin takarar kujerar gwamna da aka gudanar cikin kananan hukumomi 20 na jihar Legas da aka gudanar a yau Talata.

Na nan tafe: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mu na ci gaba da godiya a yayin kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng