Dakarun rundunar Sojan kasa sun gudanar da muhimmiyar atisaye a dajin falgore

Dakarun rundunar Sojan kasa sun gudanar da muhimmiyar atisaye a dajin falgore

Sabbin kuratan rundunar Sojan kasa ta Najeriya, rukuni na 77 sun gudanar da wata rawar daji a dajin falgore dake jahar Kano inda suka gwada dabarun yaki da aka koya musu a cibiyar horas da kuratan Sojan kasa dake garin Zaria.

Legit.ng ta ruwaito hukumar cibiyar Depot Zaria tare da hadin gwiwar kwalejin horas da mayakan sojan kasa, kwalejin horas da Sojojin Najeriya akan sarrafa makamai ne suka shirya ma kuratan wannan atisaye don saba musu da yanayin aiki da halin bada agajin gaggawa.

KU KARANTA: Jami’an tsaro sun garkame dakin taron da PDP zata fitar da dan takarar gwamna a Kano

Dakarun rundunar Sojan kasa sun gudanar da muhimmiyar atisaye a dajin falgore
Dakarun rundunar Sojan kasa
Asali: Facebook

Babban hafsan sojan kasa, Laftanar janar Tukur Yusuf Buratai ne ya kaddamar da wannan atisaye, inda ya samu wakilcin shugaban horaswa da ayyuka na musamman, Manjo Janar Lamidi Adeosun.

A nasa jawabin, kwamdan cibiyar horas da kurata Soji dake Zaria, Manjo janar Victor Ezugwu ya bayyana muhimmancin wannan rawar daji ga Sojoji, inda yace an shirya shi ne don kawar da tsoro daga zukatan Sojojin a yayin da suka shiga filin daga.

Daga karshen rawar daji, wakilin shugaban hafsoshin Sojin Najeriya ya kaddamar da aikin tallafa ma al’ummar kauyen Gada biyu da magunguna, inda da dama daga cikin marasa lafiya dake garin suka samu magunguna kyauta.

Dakarun rundunar Sojan kasa sun gudanar da muhimmiyar atisaye a dajin falgore
Dakarun rundunar Sojan kasa
Asali: Facebook

Daga cikin manyan bakin da suka halarci wannan atisaye akwai wakilin kaakakin majalisar dokokin Najeriya, dan majalisa mai wakiltar Tudunwada a majalisar wakilai, Ado Alhassan Doguwa, kwamishinan ruwa na jahar Kano, Usman Sale, wakilin Sarkin Kano Aliu Umar Dan Amar da sauran manyan Sojoji.

Dakarun rundunar Sojan kasa sun gudanar da muhimmiyar atisaye a dajin falgore
Dakarun rundunar Sojan kasa
Asali: Facebook

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa za ta koma LEGIT.ng Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel