Masu gudu sun dawo: Bala Kaura, tsohon ministan Abuja ya zama dan takarar gwamna a PDP

Masu gudu sun dawo: Bala Kaura, tsohon ministan Abuja ya zama dan takarar gwamna a PDP

Masoya tsohon ministan Abuja, Bala Mohammed, a garin Bauchi sun shiga murna da faricncikin lashe zaben zama dan takarar gwamna a karkashin jam’iyyar PDP da ya yi.

Tsohon ministan ya samu kuri’u 1,335 yayin da mai biye masa, Sanata Abdul Ningi ya samu kuri’u 802, sai kuma Sanata Adamu Ibrahim Gumba da ya zo na uku da kuri’u 15.

Tsohon ministan na daga cikin mutanen da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ke tuhuma da almundahana da dukiyar al’umma. Bayan ministan, hukumar EFCC na tuhumar daya daga cikin ‘ya’yansa da laifin mallakar kudi da kadarori ta haramtacciyyar hanya.

Masu gudu sun dawo: Bala Kaura, tsohon ministan Abuja ya zama dan takarar gwamna a PDP
Bala Mohammed
Asali: Getty Images

Da yake bayyana sakamakon zabenda safiyar yau, Litinin, a Otal din Zaranda dake Bauchi, shugaban gudanar da zaben da jam’iyyar PDP ta turo jihar Bauchi, Cif Dan Osi Orbih, ya yabawa daliget bisa da’a da hakurin da suka nuna domin ganin sun zabi mutumin da zai yiwa PDP takarar gwamna a jihar.

DUBA WANNAN: Najeriya ce hedkwatar fatara da talauci ta duniya - Jonathan

Kazalikia ya yabawa shugaban kwamitin shirya zaben a jihar Bauchi, Abdu Hassan, bisa nasarar da aka samu ta gudanar da zaben cikin natsuwa da kwanciyar hankali.

Tun da farko, PDP ta ki tantance Mohammed Auwal Jatau, dan takara na hudu da ya sayi fam din takarar gwamna a jam’iyyar bisa zarginsa da daina shiga sabgogin PDP tun shekarar 2015 da dan takarar APC ya kayar da shi a zaben gwamna.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel