An kashe wani matashi da ya nuna farin cikinsa da kisan da yan ta’adda suka yi ma janar Alkali a garin Jos
Azal ta fada ma wani dalibin jami’ar Jos dake aji uku kuma wanda ya fito daga kabilar Berom ta jahar Filato inda aka kashe shi kwana daya bayan yayi alkawarin ba za’a taba samun zaman lafiya a jihar Filato ba, inji rahoton jaridar Sahara reporters.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito matashoin mai suna Kums Shedrach ya gamu da ajalinsa a ranar Lahadi, 30 ga watan Oktoba a hannun wasu yan bindiga da suka bindigeshi a rukunin dakunan dalibai na jamiar Jos.
KU KARANTA: Najeriya ta cika shekaru 58 da samun yancin kai: Jerin shuwagabanninta tun daga 1960
Yan bindigan wanda har yanzu ba’a san ko su wanene ba sun halaka Shedrach ne kwana daya bayan ya wallafa wani rubutu a shafinsa na kafar sadarwar zamani ta Facebook inda yace duk masu son ganin zaman lafiya a Filato ba zasu samu nasara ba.
A cikin wannan rubutu da yayi, Shedarach yayi kira da a cigaba da kashe kashe a Jos har sai sun rama adadin barnar da aka musu abinda ya kira da ‘Balance of terror’ a turance, har ma yayi alwashin cewa idan ma zai mutu a wannan hanyar babu komai.
Shedrach yayi wannan rubutu ne don nuna farin cikinsa da kisan wani babban sojan Najeriya, kuma shugaban kudi da mulki na rundunar Sojan kasa, Manjo janar I B Alkali da ake zargin yan ta’addan kabilar Berom ne suka kashe shi akan hanyarsa ta zuwa Bauchi.
Wannan zargi ya kara karfafa ne bayan jami’an rundunar Sojan kasa sun kwashe ruwan wani korama dake garin Du, garin da kabilar Berom suka mamaye, inda suka gano motar mamacin da wasu kayansa, tare da wasu motoci guda hudu na daban.
Wannan ne yasa Sojoji ke ganin yan ta’addan kabilar Berom ne suka kashe janar Alkali, sa’annan suka boye motarsa a cikin koramar, kamar yadda suka kashe wasu mutane suka boye motocinsu a cikin ruwan, musamman ta yadda matan garin suka gudanar da zanga zangar nuna rashin amincewa da Sojoji su taba wannan ruwa.
Amma kwamishinan Yansandan jahar, Undie Udie yayi kira ga dukkanin bangarorin biyu dasu maida wukakensu, kuma kowa ya tsagaita, sa’annan yayi kira ga jama’an dake kauyen dalibai, hanyar Bauchi, Angwan rukuba, da Rikkos dasu kasance a cikin gidajensu ba fita.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa
Mungode da kasancewanku tare da mu
Asali: Legit.ng