Shugaban kasar Koriya ta Arewa na rubuto min wasikar soyayya - Donald Trump

Shugaban kasar Koriya ta Arewa na rubuto min wasikar soyayya - Donald Trump

Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewar soyayya ta kullu tsakaninsa da takwaransa na kasar Koriya ta Arewa, Kim Jong Un, har ta kai ga sun fara musayar wasikun kaunar juna.

A jiya, Asabar, ne shugaba Trump ya kara yabon Kim a bainar jama'a, yayin wani taron jam'iyyar Republican a jihar West Virginia ta kasar Amurka.

Shugaban kasar Koriya ta Arewa na rubuto min wasikar soyayya - Donald Trump
Shugaban kasar Koriya ta Arewa na rubuto min wasikar soyayya - Donald Trump
Asali: Depositphotos

DUBA WANNAN: Jam'iyyar PDP: Saraki ya maka Atiku da Tambuwal da kasa a zaben jin ra'ayi

"Tabbas soyayya ta kullu tsakanin mu, yana rubuto min wasiku masu matukar kyau," Trum ya shaidawa jama'ar da suka halarci taron gangamin na jiya.

A baya dai an dade ana nuna yatsa da musayar kalamai marasa dadi tsakanin shugabannin biyu.

Rashin jituwa ta shiga tsakanin Kim da Trump ne a kan mallakar makamin kisan kare dangi mai linzami.

Ko a shekarar da ta gabata sai da shugaba Trump na Amurka ya yi barazanar rushe kasar Koriya ta Arewa, lamarin da ya sa shugaba Kim ya kira shi da "mai tabin hankali".

A watan Yuni ne shugabannin biyu suka hadu, a karo na farko, a kasar Singapore domin tattauna yadda zasu cimma matsaya a kan batun mallakar makami mai linzami.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel