Gwamnatin Kano da ta Misra zasu yi sabuwar Abbatuwa a Kano
- Gwamnatin jihar Kano da Kamfanin Bovine Masters zasu bude katafaren gidan nama a jihar
- Kashi na farko na aikin zai lashe dala miliyan 12
- Aikin zai samar da halastattun nama ne don amfanin gida da waje

Asali: Depositphotos
Gwamnatin jihar Kano tare da kamfanin Bovine Masters na Egypt, sun kammala shirye shiryen samar da kamfanin samar da nama na miliyoyin daloli a jihar.
Ana sa ran kashi na farkon aikin zai lashe dala miliyan 12, wanda zai kunshi sarrafa naman shanu da kananan dabbobi tare da siyarwa, kamar yanda Gwamna Abdullahi Ganduje ya fada.
DUBA WANNAN: Zamu ci gaba da kula da ECOWAS - Buhari
Kamar yanda Darakta Janar na yada labarai da sadarwa, Ameen Yassar ya fada, gwamnan yace, "Aikin zai samar da halastattun nama domin amfanin gida da kuma kasuwannin wajen kasar a Afirka ta arewa"
Kari da cewa, za'a hada guiwa da cibiyoyin da ke samar da abincin Halal dake fadin jihar.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng