Ya zuwa yanzu gwamnatin APC ta tayar da komadar kamfunnan takin zamani 18
- An yaba wa gwamnatin APC kan cika alkawari
- Gwamnatin nan tayi alkawarin farfado da noma
- Ta samar da taki da jari ga manoma

Asali: UGC
Hadakar kungiyoyin masu samar da takin zamani, wadanda a turance ake kira da Fertiliser Producers and Suppliers Association of Nigeria, FEPSAN, sun ce a wannan gwamnatin ta APC, an sami habakar samar da takin zamani har a karkashin shirin Presidential Fertiliser Initiative, PFI, wanda gwamnatin tarayya ta samar.
A shirin, a cewar shugaban kungiyar, Thomas Etuh, a zantawarsa da manema labaru a Abuja, yace an farfado da akalla manyan kamfunnan samar da takin a fadin kasar nan, har 18 tun bayan hawan shugaba Muhammadu Buhari gadon mulki.
DUBA WANNAN: Rikici a Jos ya hallaka 14
Ya kara da cewa, cikin kamfunnan 32 da ake dasu a kasar nan, a da kafin 2015, 6 ne kawai ke aiki shima kuma na marga-,arga, bacci gyangyadi, amma yanzu da aka tayar da 18, an sami habakar kayan aikin gona, don haka yana sam-barka.
Ya kara da cewa, ana duba yiwuwar tayar da komadar wasu biyar din, sannan kuma akwai shirin kera guda biyar sabbi a fadin kasar nan.
Ya zuwa yanzu, a cewarsa, akwai masana'antun a Zamfara, Ajaokuta ta Kogi, Akwa-Ibom da Funtua a Katsina State, sai ta Kaduna wadda ake shirin budewa kwanan nan.
A hasashensa ma, yace za'a iya samun damar fitar da wasu nau'ukan na takin zamanin zuwa kasashen ketare nan da badi in abubuwan suka tabbata.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng